Ortom Ga Buhari: Mutuncinka Ya Zube, Ka Kwashe Shi Ta Hanyar Gyara Shi Ta Hanyar Gyara Tsaro

Ortom Ga Buhari: Mutuncinka Ya Zube, Ka Kwashe Shi Ta Hanyar Gyara Shi Ta Hanyar Gyara Tsaro

  • Gwamnan jihar Benue ya sake caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu cikin makon nan
  • Ya ce, mutuncin Buhari ya zube, kuma hanya daya ta kwashe shi shine ya gyara bangaren tsaron Najeriya
  • Gwamna Samuel Ortom na yawan sukar yadda harkokin kasar nan ke tafiya karkashin jagorancin Buhari

Makurdi, jihar Benue - Gwamnan Saumuel Ortom na jihar Benue ya shawaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kwashe mutuncinsa da zube ta hanyar magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.

Kalaman na Ortom na zuwa ne bayan fitar wata sanarwa da aka danganta ga hadimin Buhari, Garba Shehu, ranar Laraba 31 ga watan Agusta, TheCable ta ruwaito.

Gwamnan Benue ya caccaki Buhari
Ortom ga Buhari: Mutuncinka ya zube, ka kwashe shi ta hanyar gyara shi ta hanyar gyara tsaro | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Garba Shehu ya ce Ortom na siyasar karnakanci lokacin da ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya na kokarin lallasa kokarin magance rashin tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Zargi Gwamnan PDP da Yi wa Duniya Karya Kan Batun Tsaro

A cikin wata sanarwa a yau Alhamis 1 ga watan Satumba, Nathaniel Ikyur, sakataren yada labarai na Ortom, ya naqalto gwamnan na cewa duk lokacin da ya soki barnar mulkin Manjo Buhari yadda matsalar tsaro ta lalace, hadiman Buhari na caccakar batunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Don haka, gwamnan ya ce, idan har abubuwan da yake fadi game da gwamnatin Buhari ba gaskiya bane, to ya kamata gwamnati ta nunawa 'yan Najeriya irin ayyukan da ta tabuka a fannin tsaro.

Garba Shehu miyarsa yake gyarawa, inji Ortom

A kalamansa:

“Abin takaici ne ganin yadda irin su Garba Shehu ke nuna rashin tausayi ga iyalan wadanda ‘yan ta’addan Fulani ke kashewa a kullum.
“Matukar suka cika aljifansu, cewa shugaban kasa suke ya tafi ya kwanta kawai tare da ce masa komai na tafiya lafiya.
“Garba dai mutum ne da biyayyarsa ta ta'allaka da kudi. A yau yana ririta shugaban kasa ne domin shi ne tushen rayuwarsa a halin yanzu."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Gwamnan PDP Ya Ce Boko Haram Na Shirin Fara Kai Hare-Hare A Jiharsa

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Buhari ta takura wasu kungiyoyin fafutuka irinsu IPOB amma kuma tana lallaba Fulani 'yan ta'adda, rahoton Daily Post.

Gwamnan ya sha zargin Fulani makiyaya da ayyukan ta'addanci a kasar nan, musamman sace mutane da dabbobinsu.

Idan Siyasa Ƙazamin Harka Ne, Kiristoci Su Shiga Daga Ciki Su Tsaftace Shi, In Ji Babban Limamin Coci

A wani labarin, dan takarar kujerar sanata na jam'iyyar APC a Benue South, Kwamred Daniel Onjeh, a jiya ya ziyarci zababen Archbishop na cocin Methodist, Archibishop Oliver Abah, a gidansa da ke Otukpo, jihar Benue.

Archbishop Abah ya tarbi Onjeh da tawagarsa tare da wasu manyan limaman cocin na Methodist kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Da ya ke magana a wurin taron, Onjeh ya ce ya yi murnar jin labarin nadin Archbishop Abah a matsayin zababen Prelate na Cocin Methodist na Najeriya.

Kara karanta wannan

Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi

Asali: Legit.ng

Online view pixel