2023: Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game da Atiku da Kwankwaso

2023: Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game da Atiku da Kwankwaso

  • Bola Tinubu bai shahara a matakin zaɓen kasa ba idan aka kwatanta shi da yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun PDP, NNPP da LP
  • Mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa maso yamma, Dr. Salihu Lukman, shi ne ya ayyana amince wa da batun
  • Salihu Lukman yace wannan batun gaskiya ne kuma ɗaya daga cikin kalubalen APC game da shirye-shiryen Kamfe

Abuja - Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa reshen shiyyar arewa maso yamma, Salihu Lukman, ya amince da gaskiyar cewa Bola Tinubu, ba wani sananne bane idan ana batun zaɓen shugaban kasa a Najeriya.

A wata hira ta bayan fage da Jaridar This Day, Lukman ya bayyana cewa karo na karshe da Tinubu ya fito a takardar kaɗa kuri'a shi ne a zaɓen 2003 ba kamar Atiku Abubakar, da Peter Obi ba.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Zai Haɗa Karfi da Atiku, Gaskiya Ta Fito

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
2023: Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game da Atiku da Kwankwaso Hoto: Bola Tinubu/facebook
Asali: Facebook

A wurinsa, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, da na jam'iyyar NNPP da Labour Party sun shahara a siyasar ƙasa da zabukan mataki lamba ɗaya in banda Tinubu, hakan ba ƙaramin kalubale bane ga APC.

A kalamansa, Lukman ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan kalubale ne ga Demokaraɗiyya, ba APC kaɗai aka ware ba ko PDP, lamarin ya shafi dukkan jam'iyyun siyasa. Ka je ka bincika, musamman a matakin kujera lamba ɗaya, muna cikin yanayin da fuskokin sauran 'yan takara sanannu ne a zaɓe."
"Ɗan takara ɗaya da zaka zare shi ne na mu na jam'iyyar APC, karo na karshe da ya fito a takardar kaɗa kuri'a shi ne a shekarar 2003 kuma tun daga wannan lokaci bai sake fito wa a zaɓe ba."
"Amma ba shi ne matsalar ba, aƙalla 'yan takarar shugaban ƙasa na fitattun jam'iyyu uku da ake gani suna sahun gaba, PDP, NNPP da Labour Party, ɗan takarar LP ya shiga zaɓe a 2019. Ina tunanin waɗan nan ne matsalolin mu."

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Bola Tinubu Da Jiga-Jigan APC Sun Nemi Wata Alfarma Ɗaya Daga Wurin Jonathan

Jigon APC ya yi wannan kalaman ne yayin da yake amsa tambayar yadda jam'iyyarsa ke shirin gudanar da yaƙin neman zaɓe gabanin 2023.

An Faɗa Mun wanda zai gaji Buhari - Malami

A wani labarin kuma Wani Babban Malami Ya Bayyana Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023, Yace Sako Ne Daga Allah

Wani Malami ya bayyana maganar Manzanci cewa ɗan takarar APC, Bola Tinubu, ne zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023.

A shekarar 2019, Malamin Cocin ya yi hasashen shugaba Buhari zai lashe zaɓe karo na biyu, haka Sanata Omo-Agege.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262