Dalilan da suka Jawo Tinubu da Gwamnoni 5 Suka Ziyarci Jonathan Sun Farawa Fitowa
- Bola Ahmed Tinubu mai neman takara a APC ya je gidan Dr. Goodluck Jonathan tare da Sanata Kashim Shettima a garin Abuja
- Bayanai sun fito game da abin da ya kai ‘yan takaran da wasu Gwamnonin jam’iyyar APC zuwa gidan tsohon shugaban kasa
- Wata majiya tace ana sa Jonathan cikin wadanda suka saye fam din takaran APC a 2023, kuma cikakken ‘dan jam’iyyar APC ne
Abuja - ‘Dan takaran shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima sun yi takakiyya zuwa wajen Goodluck Jonathan.
Majiyoyin Daily Trust sun yi mata bayanin abin da ya sa aka ga tawagar Tinubu a gidan Goodluck Jonathan wanda ya yi mulki na shekaru biyar a inuwar PDP.
Rahotanni sun tabbata cewa ‘yan takaran da wasu gwamnonin APC sun ziyarci tsohon shugaban kasar ne agidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Talata.
Wani daga cikin makusantan ‘dan takaran na jam’iyya mai mulki yace an zauna da Jonathan ne a matsayinsa na wanda ya taba rike shugabancin kasa a baya.
Jonathan ma 'dan takara ne
Baya ga haka, Jonathan yana cikin wadanda aka saye fam a APC na shiga takarar shugaban kasa da sunansa, duk da bai je wajen tantance masu neman takara ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baya ga haka, Jonathan cikakken ‘dan jam’iyyar APC ne wanda yake da rajista a jihar Bayelsa.
Tikitin Musulmi-Musulmi a APC
Rahoton da aka fitar ya kuma bayyana cewa abin da aka tattauna shi ne yadda za a tallata tafiyar Tinubu-Shettima, ganin dukkanin ‘yan takaran Musulmai ne.
“A yanzu Tinubu da magoya bayansa sun fara yin zama da mutanen da kiristoci ne da nufin nuna masu fa’idar zaben Musulmi da Musulmi a 2023.”
- Majiya
Yadda taro ya kasance
Wani wanda ya san abin da ya wakana a wajen taron na ranar Talata, ya fadawa jaridar cewa tsohon shugaban kasar ya karbi ‘ya ‘yan na APC hannu biyu-biyu.
Irinsu Femi Fani-Kayode wanda yanzu ya tsallako zuwa jam’iyyar APC, ya yabi Jonathan a kan yadda ya karbi Tinubu da Shettima cikin girmamawa da farin ciki.
Reno Omokri ya tuna yadda Tinubu ya rika sukar gwamnatin Jonathan tsakanin 2010 zuwa 2015, sai ga shi yanzu ana zargin sun je kamun kafar siyasa wajensa.
Gwamnatin hadaka a 2023
A baya kun samu labari cewa 'dan takaran shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya yi alkawarin bin salon Shugaba Ummaru Yar’adua domin hada-kan al’umma.
Yayin da ya hangi 2023, ‘Dan takaran na PDP watau Wazirin Adamawa yace zai iya kafa gwamnatin hadaka da sauran ‘ya ‘yan jam’iyyun hamayya idan ya ci zabe.
Asali: Legit.ng