An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku
- Wani jigo a jam’iyyar PDP yana so a karbe tikiti daga hannun Atiku Abubakar, a tsaida masu Gwamna Nyesom Wike
- Gwamnan Ribas ya zo na biyu a zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP, bai samu tutar takarar shugabancin kasa ba
- Da aka shiga kotun tarayya na Abuja, Lauyan da yake kare wadanda ake tuhuma ya roki Alkali ya kara masa lokaci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - A ranar Laraba, 14 ga watan Satumba 2022, babban kotun tarayya da ke aiki a garin Abuja zai saurari karar da aka shigar a kan tikitin PDP a 2023.
The Nation ta kawo rahoto dazu cewa Alkali Ahmed Mohammed ya zabi wannan rana domin ya cigaba da sauraron karar bayan an nemi karin lokaci.
Lauyan da ta tsayawa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP, Prisicila Eje ce ta bukaci kotu ta kara masa lokaci.
Ganin Lauyan da ya shigar da kara, Wilfred Okoi bai da ja a kan wannan bukata, Mai shari’a Ahmed Mohammed ya amince a dawo nan makonni biyu.
Barista Wilfred Okoi bai da ja
Wilfred Okoi ne yake tsayawa Prince Michael Ekamon da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, suna kalubalantar wanda aka ba takarar shugaban kasa a PDP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A farkon watan Yuli aka fara shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022, ana rokon kotun tarayyar ta hana Atiku tsayawa takara a 2023.
Rahoton yace hukumar INEC ba ta iya turo Lauyan da ya kare ta a zaman kotun da aka yi yau ba.
Bukatar Lauyan da ya kai kara sun hada da ayyana Gwamna Wike a matsayin asalin ‘dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.
Matsayar Atiku, Tambuwal da PDP
Jaridar The Guardian tace Okoi ya fadawa kotu cewa jam’iyyar PDP, Gwamna Tambuwal da Atiku da ake kara sun kalubalanci rokon da ya gabatar.
Duk da Wike ya yi ikirarin babu hannunsa a wannan kara da ke kotu, Lauyan da ya wakilci Gwamnan da kuma jagoran jam'iyyar PDP bai nuna haka ba.
Atiku ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP, amma masu korafi suna ganin ya yi galabar ne bayan Tambuwal ya janye masa duk lokaci ya kure.
Wike ya ji haushin Atiku
Kwanakin baya kun ji labari Nyesom Wike yana ganin Aminu Tambuwal ya sallamawa Atiku Abubakar kuri’unsa ne bayan fara gudanar da zabe.
A zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasan PDP ta shirya, sai a mintin karshe aka ji Tambuwal ya marawa Atiku baya, wannan abin ya fusata Wike sosai.
Asali: Legit.ng