Atiku Abubakar Ya Yi Alkawarin Bin Salon Yar’adua Domin Hada-kan 'Yan Najeriya

Atiku Abubakar Ya Yi Alkawarin Bin Salon Yar’adua Domin Hada-kan 'Yan Najeriya

  • Da alama Atiku Abubakar yana kokarin kwadaito jama’a yayin da ya hango kujerar shugaban Najeriya a zaben 2023
  • Atiku Abubakar ya yi alkawarin zai tafi da ‘yan sauran jam’iyyu a gwamnatinsa muddin ya yi nasarar zama shugaban kasa
  • ‘Dan takaran na PDP yana ganin hakan zai kawo zaman lafiya da hadin-kai, wanda zai jawo bunkasar tattalin arziki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Atiku Abubakar mai neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP, yana tunanin kafa gwamnatin hadaka a Najeriya.

Jaridar This Day tace Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar da kan shi bayan ya gama zantawa da gungun mutane a Kano.

‘Dan takaran na jam’iyyar PDP yace gwamnatinsa za ta tafi da kowa a Najeriya domin ganin an hada-kan al’ummar kasa, tare da magance matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

‘Dan gwagwarmaya Ya Fadawa Atiku, Obi da Kwankwaso Hanyar Doke Tinubu a Saukake

A ganin Atiku, tafiya da kowane bangare a cikin gwamnatinsa, zai rage zafin sabani a Najeriya.

Gwamnatin hadin-kai

“Akwai batun la’akari da kafa gwamnatin hadin-kai da zai rage zafin rabuwar kai, ya hada-kan ‘yan Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kuma ya kawo ingantar halin tsaro. Idan aka samu tsaro, kudi za su shigo, saboda haka tattalin arziki zai bunkasa.”
Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Kano Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Da yake jawabi a ranar Talata, mai neman kujerar shugaban kasar ya dauki lokaci yana tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar tattalin arzikin kasa.

Wazirin Adamawa yace idan aka samar da tsaro, tattalin arziki zai bunkasa ta hanyar tatsar haraji da kyau, da kuma jawo masu hannun jari daga kasashen waje.

Rahoton Premium Times yace Atiku ya soki yawan bashin da gwamnatin Muhammadu Buhari take ciki, yace ana boye gaskiyar halin da kasa take ciki.

Kara karanta wannan

2023: An Sanya Lokacin Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP, Atiku Zai Fara Zawarcin Wasu Yan Siyasan Kano

Gwamnatin hadin-kai a Najeriya

A baya an taba jarraba irin wannan gwamnati ta hadin-kai a Najeriya wanda za a ba ‘ya ‘yan jam’iyyun hamayya mukamai duk da ba da su aka lashe zabe.

Legit.ng Hausa za ta iya tunawa Marigayi Umaru ‘Yar’adua ya yi wa ‘yan adawa tayi a gwamnatin tarayya, ya ba wasu ‘yan jam’iyyar ANPP da PPA Ministoci.

Watakila Atiku ya raba mukamai ga jam'iyyu irinsu LP, NNPP ko APC idan ya ci zabe.

PDP ta karbe Shekarau

Ba a je ko ina ba, aka ji labari tsohon Gwamnan Kano watau Ibrahim Shekarau ya saki tafiyar Rabiu Kwankwaso, ya shiga jirgin Atiku Abubakar a PDP.

A jiya Rabiu Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya jawo NNPP ta rasa Malam Shekarau, duk an ba shi takarar ‘Dan Majalisar Dattawa a zabe na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng