Mutumin da ya nemi ya birkita zaben 2015 saboda Jonathan, ya koma Jam’iyya APC

Mutumin da ya nemi ya birkita zaben 2015 saboda Jonathan, ya koma Jam’iyya APC

  • Ta tabbata Mista Elder Godsday Peter Orubebe ya zama cikakken ‘dan jam’iyyar APC a Najeriya
  • Elder Godsday Peter Orubebe shi ne ya nemi ya kawo hatsaniya lokacin tattara kuri’un zaben 2015
  • Tsohon Ministan kasar ya yi alkwarin za a rika damawa da mutanensa yanzu a gwamnatin sama

Delta - Elder Godsday Peter Orubebe wanda ya taba rike Minista a gwamnatin tarayya, ya shiga jam’iyyar APC mai mulki bayan ficewarsa daga PDP.

Rahoton PM News ya tabbatar da cewa Elder Godsday Peter Orubebe ya sauya-sheka ne bayan abin da ya kira rashin tanadin PDP na karbe mulki.

Da yake yi wa ‘ya ‘yan APC na kasar Ijaw jawabi a ranar Juma’a, 1 ga watan Yuli 2022, ‘dan siyasar ya shaidawa Duniya ya yi rajisa da APC a jihar Delta

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan APC Da Ake Rade-Radin Zai Fita Daga Jam'iyyar Ya Yi Karin Haske

Bugu da kari, an rahoto Peter Orubebe yana cewa zai yi wa APC kokari wajen ganin duka ‘yan takaranta biyar sun yi nasara a zaben da za ayi a 2023.

Orubebe ya ce sai inda karfinsa ya kare musamman domin tabbatar da ‘yan takara uku da jam’iyyar ta tsaida a karamar hukumar Burutu sun yi nasara.

An ji tsohon Ministan na Neja-Delta yana cewa zai yi tanadin duk abin da ake bukata a ci zabe. Kafin yanzu ya rike kujerar Kansila a gwamnatin PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Orubebe ya koma Jam’iyya APC
Nyesom Wike tare da su Elder Orubebe Hoto: naijaonpoint.com
Asali: UGC

Daily Post ta rahoto Orubebe yana kokawa a kan yadda mutanen yankinsa na jihar Delta suka gagara samun mukami masu tsoka a gwamnatin tarayya.

An ji Orubebe ya sha alwashin cewa daga yanzu za a rika damawa da mutanen Ijaw a gwamnatin tarayya, tun da har ya zabi ya shiga jirgin jam’iyya mai iko.

Kara karanta wannan

Jerin manya 6 da suka yi wa Peter Obi mugun baki, su ka ce ba zai mulki Najeriya a 2023 ba

APC ta shiga Ijaw

Shugaban APC na karamar hukumar Burutu, Moni Seikemienghan Moni, ya godewa ‘dan siyasar saboda ya zabi ya shigo jam’iyyarsu ta APC a wannan lokaci.

Kwamred Moni Seikemienghan Moni yake cewa samun irin Orubebe, babban cigaba ne ga jam’iyyar, domin ba ta da karfi a yankin Ijaw a Neja Delta.

“Kasar Ijaw ta samu babban ‘dan siyasa da ake ji da shi, wanda zai cike gibin da ake da shi.”

- Moni Seikemienghan Moni

Tinubu zai gamu da kalubale?

A makon nan ne aka ji labari wani jagora a jam’iyyar APC daga Kudancin Najeriyaya yi watsi da batun sak, ya ce shinkafa da wake zai yi a babban zaben 2023.

Tsohon mataimakin gwamnan Imo, Jude Agabos yace tun da har aka ba Asiwaju Bola Tinubu tikiti, Peter Obi na jam’iyyar LP zai ba kuri'arsa ba wai APC ba.

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu Kwankwaso ya zama Mataimakin Peter Obi idan an hade ba inji Jibrin

Asali: Legit.ng

Online view pixel