Zan siyar da kaso 90 na NNPC idan aka zabe ni – Atiku ya sha alwashi
Dan takarar kujeran shugaban kasa Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya ce zai siyar da kaso 90 na kamfanin man fetur din Najeriya sannan ya bar wa gwamnatin tarayya kaso 10.
Atiku ya bayyana hakan a wani hira da The African Report.
Atiku wanda ya jagoranci kungiyar kamfanoni masu zaman kansu wato National Council on Privatisation lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa yace ya kamata ace NNPC ya fi samun riba a yanzu.
Dan takarar shugaban kasar yace kamata yayi ace Najeriya na samar da mai sama da ganga miliyan biyu a kowace rana.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin hutu
Da yake ci gaba da Magana kan siyar da kamfanin man kasar, yace, “idan har ba wai ana aiki bane a koda yaushe, toh kamfanonin man fetur da gas za su fuskanci kalubale wajen zuba jari sosai a Najeriya.
“A lokacin da muka gabatar da sabon doka. Muna sanya ran cewa Najeriya zata iya fitar da gangar mai kusan miliyan hudu a kowace rana, amma muna nan har yanzu, muna samar da gangar mai kasa da miliyan biyu a rana."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng