Ba zan bar Shugaba Buhari ba, kuma bazan yi takara da shi ba inji Bola Tinubu

Ba zan bar Shugaba Buhari ba, kuma bazan yi takara da shi ba inji Bola Tinubu

- Asiwaju Bola Tinubu yace ba zai taba goyon bayan Atiku ba

- Tsohon Gwamnan Legas yace yana tare da Shugaba Buhari

- Babban ‘Dan siyasar ya karyata rade-radin cewa zai bi Atiku

Tsohon Sanata kuma Gwamnan Jihar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yace ba zai taba goyon bayan takarar Shugaban kasar Wazirin Adamawa watau Alhaji Atiku Abubakar ba kamar yadda wasu ke radawa cikin kwanakin nan a Kasar.

Ba zan bar Shugaba Buhari ba, kuma bazan yi takara da shi ba inji Bola Tinubu
Bola Tinubu yace babu maganar ya goyi bayan Atiku

Jaridar Sun ta rahoto cewa babban Jigon na Jam’iyyar APC mai mulki Bola Tinubu yace yana tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari muddin zai tsaya takara kuma a zaben 2019. Tinubu yace kuma ba zai yi takara da Shugaba Buhari ba.

KU KARANTA: Abin da ke hana 'Yan Arewa shiga gidan Soja - Inji Minista

Ba zan bar Shugaba Buhari ba, kuma bazan yi takara da shi ba inji Bola Tinubu
Shugaba Buhari zan yi ba Atiku ba inji Bola Tinubu

Babban ‘Dan siyasar Kasar ya karyata rade-radin cewa yana tare da Atiku Abubakar wanda ya bar APC a watan jiya. Tinubu yace babu abin da zai sa ya bar ‘Dan takarar sa a APC ya kama wani dabam a Jam’iyyar adawa a zabe mai zuwa.

Tinubu yayi wannan jawabi ne ta bakin wani Hadimin sa Tunde Rahman. Tinubu wanda ya taka rawar gaske wajen ganin Buhari ya dare mulki a 2015, yace Shugaban na kokarin shawo kan kalubalen kasar nan ne don haka shi kam yana bayan sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: