Bamu Zo Nan Don Shan Jar Miya Ba, Mun Zo Ne Don Yiwa ’Yan Najeriya Abinda Ya Dace, Inji Tinubu

Bamu Zo Nan Don Shan Jar Miya Ba, Mun Zo Ne Don Yiwa ’Yan Najeriya Abinda Ya Dace, Inji Tinubu

  • Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana abin da ya shirya yiwa 'yan Najeriya, da kuma irin kiran da ya amsa
  • 'Yan takarar shugaban kasa a Najeriya na ci gaba da tallata manufofinsu na gaje Buhari a zaben 2023 mai zuwa
  • Tinubu ya gana da wasu jiga-jigan siyasar Najeriya a birnin Landan, inda suka tattauna makomar siyasa

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga alherin da ya tanadarwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari.

Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce sam bai shirya zuwa Villa domin ya mike kafa ya sharbi jar miya ba, zai zo ne dan yiwa 'yan Najeriya aikin da ya cancanta.

Tinubu ya fadi tanadinsa ga 'yan Najeriya a zaben 2023
Bamu Zo Nan Don Shan Jar Miya Ba, Mun Zo Ne Don Yiwa ’Yan Najeriya Abinda Ya Dace, Inji Tinubu | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Depositphotos

A wani sako da ya yada a shafinsa na Twitter, Tinubu ya bayyana, cewa an kira shi ya tsaya takara ne saboda kaunar da yake yiwa kasar nan da kuma ayyukan da ya sa a gaba gareta.

Kara karanta wannan

2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba mu zo nan don shan romo ba. Mun zo ne don yin abin da ya dace ga mutane da kasarmu.
"Mun zo nan ne don amsa wata kira mai girma, mai girma ainun. Wannar kiran dai itace kaunar Najeriya. Ba mu kuskura mun yi wasa da wannan damar ba saboda ba lallai mu iya samun wata ba."

Wannan kalami na dan takarar shugaban kasa a APC na zuwa ne jim kadan bayan dawowarsa daga Landan, inda ya gana da wasu jiga-jigan siyasar Najeriya.

Sakamakon ganawar Tinubu da 'yan siyasar Najeriya a Landan bai zama batun siyasa zalla ba, an tattauna kan abubuwan da suka shafi makomar Najeriya, inji gwamnan Ribas Nyesom Wike.

Bai Kamata a Bar Lamarin Tsaro Ga Kashim Shettima Ba, Inji Jigon Jam’iyyar PDP

A wani labarin, jigon jam'iyyar PDP ya hango matsala, ya gargadi 'yan Najeriya da su kula da gamin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

Anthony Ehilebo, ya shawarci 'yan Najeriya da cewa, kada su bari Kashim Shettima ya kusanci kujera a Villa, don kada ya kula da lamurran tsaro a Najeriya.

Jigon na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna na shirin Politics Today na Channels Tv a ranar Lahadi, 28 ga watan Agustan bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel