2023: Cikakken Bayanin Yadda Tinubu Ya Ki Amincewa Da Bukatun Wike A Landan Ya Bayyana

2023: Cikakken Bayanin Yadda Tinubu Ya Ki Amincewa Da Bukatun Wike A Landan Ya Bayyana

  • An rahoto cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya ki amincewa da wasu bukatun gwamnan Rivers, Nyesom Wike
  • Wasu masu masaniya kan lamarin sun bayyana cewa Wike ya bukaci Tinubu ya tilastawa yan takarar gwamna na jihohin Rivers, Oyo, Abia da Benue su janye wa yan takarar PDP
  • Tinubu, a bangarensa, ya ce baya son ya yi alkawarin da ba zai cika ba, yana mai cewa zai iya duba yiwuwar hakan a jihar Rivers amma sauran za su yi wuya

An bayyana abubuwan da aka tattauna tsakanin gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinbu, rahoton This Day.

Wike, gwamnan jihar Rivers ya fusata da sakamakon zaben fidda gwani na jam'iyyarsa da kuma rashin zabinsa a matsayin abokin takara da Atiku Abubakar ya ki yi.

Kara karanta wannan

2023: Bangaren Wike Ta Bada Sunan Wanda Ta Ke So A Nada Shugaban PDP Na Kasa

Wike da Tinubu.
2023: Cikakken Bayanin Yadda Tinubu Ya Ki Amincewa Da Bukatun Wike A Landan Ya Bayyana. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Twitter

Wike na neman madafa ta siyasa bayan zaben shekarar 2023

Sakamakon hakan, Wike na neman madafa ta siyasa bayan babban zaben shekarar 2023 idan ya sauka daga mukaminsa na gwamna, hakan yasa ya rika ganawa da shugabannin jam'iyyun hamayya, ciki har da Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan Wike ya gabatar da bukatunsa, dan takarar shugaban kasar na APC ya nuna ba zai iya biya masa bukatunsa ba, sannan ya bayyana dalilin hakan.

Wasu da suka hallarci taron sun ce bukatun na Wike sun yi tsauri hakan yasa da wuya a iya cika masa.

Abin da Wike ya bukata daga Tinubu

Majiyar ta bayyana bukatar ta Wike:

"Idan ya ci zaben shugaban kasa wanda shine za a fara yi, zai tabbata ba zai tallafawa yan takarar gwamna, da majalisar dokokin jiha a jihohin Rivers, Benue, Oyo da Abia, ta yadda yan takarar da ke bangarensa da sauran gwamnonin za su ci zabe su cigaba da iko da jihohin."

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dalilin ganawar Wike da Atiku, Tinubu, Peter Obi da Obasanjo a Landan ya fito

Wike kuma yana son Tinubu ya tabbatar masa cewa za a kyalle mutanensa su ci zaben majalisar dattawa, majalisar wakilai na tarayya, da gwamnoni da ke takarar majalisa.

Wannan bukatun ba za su yiwu ba saboda za a yi zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya a lokaci guda ne.

Majiyar ta kara da cewa:

"Dan takarar na APC kawai ya ce, eh, zan iya duba yiwuwar biya masa bukatansa a Rivers, amma ba zai iya bashi tabbacin yin hakan a jihohin Oyo, Benue da Abia ba; cewa hakan zai yi wuya koma baya son ya yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba."

A cewar majiyar, Wike na son Tinubu ya tilastawa yan takarar APC na jihohin Rivers, Oyo, Abia da kuma musamman Benue su janye takararsu.

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

Kara karanta wannan

Atiku ya kade: Obasanjo ya gana da Peter Obi, Wike da wasu jiga-jigai a Landan

A wani rahoton, Cif Okhue, kakakin kungiyar Fararen Mayu da Matsafa ta Najeriya (WITZAM), ya ce babu wani matsala don jam'iyyar APC ta tsayar da musulmi biyu a takarar shugaban kasa da mataimaki.

Ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke bayyana cewa nan bada dadewa ba kungiyar za ta hango wanda zai zama shugaban kasa a 2023, Independent ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164