Za a Daure 'Yan Siyasan da Aka Samu Su Na Kamfe a Masallatai da Coci inji INEC

Za a Daure 'Yan Siyasan da Aka Samu Su Na Kamfe a Masallatai da Coci inji INEC

  • Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta ta ankarar da ‘yan takara da jam’iyyun siyasa game da dokar zabe na shekarar 2022
  • Festus Okoye yace haramun ne a rika kamfe ko bata wani ‘dan takara a masallatai, coci ko wani wurin zaman jama’a
  • Duk wani ‘dan siyasa da aka samu yana amfani da majami’ai wajen kamfe zai iya fuskantar dauri a gidan yari ko dai tarar kudi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Saura kusan wata guda a soma yakin neman zaben 2023 gadan-gadan, hukumar zabe ta INEC ta gargadi masu yin kamfe a masallatai da coci.

The Cable ta kawo rahoto cewa hukumar zabe na kasa mai zaman kanta ta ja-kunnen ‘yan siyasa kan amfani da wuraren jama’a da ibada wajen kamfe.

INEC ta yi kira ga jam’iyyu su bi abin da dokar zabe na shekarar 2022 ta fada wajen tallata ‘yan takararsu a zabukan jihohi da na tarayya da za ayi a 2023.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

Festus Okoye wanda shi ne kwamishinan wayar da kan jama’a a kan harkar zabe na INEC, ya kara yi wa ‘yan jarida fashin bakin abin da dokar zabe ta tanada.

Babu zagi da bata wani a doka

A hirar da aka yi da shi, Okoye yace doka ba ta hallata cin mutunci da zage-zage da sunan siyasa ba. Jami’in ya kafa hujja ne da sashe na 92 na dokar zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, dokar zaben ta yi bayani karara wajen haramtawa ‘yan takara a Najeriya yin kalaman da za su iya taba wani addini, kabila ko kuma wani yanki.

INEC.
Shugaban zabe na kasa Hoto: @ INECNigeria
Asali: UGC

Yin kamfe a majami’ai

Bugu da kari, Punch tace wani bangare na sashe na 92 ya hana amfani da wuraren ibada, ofisoshin ‘yan sanda da kuma wurin zaman jama’a wajen yin kamfe.

Ba a amincewa kowa amfani da masallatai ko coci wajen tallata ‘dan takara ko jam’iyya, ko cin mutuncin abokan adawa ko kuma a yada manufar siyasa ba.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Kano Sanusi ya ba 'yan Najeriya shawarin shugaban da za su zaba

Ba a yarda ayi amfani da dodanni ko duk wani mutumin da ya rufe fuskarsa a wajen yakin neman zabe ba, INEC tace duk wanda ya yi wannan, to ya saba doka.

Dabar siyasa ta saba doka

Har ila yau, Okoye ya gargadi ‘yan takara a game da amfani da ‘yan bangar siyasa da sunan maganin masu tada tsaye, yace yin hakan laifi ne da zai kai ga kotu.

Sashe na 7(a)(b) da sashe na 8 na dokar zabe sun yanke hukuncin daurin shekara ko kuma tarar N1,000,000 zuwa N2,000,000 ga 'dan siyasar da aka samu da laifi.

Shi kuma wanda ya taimaka wajen amfani da ‘yan daba a siyasa zai fuskanci daurin shekaru uku ko kuma tarar N500, 000 a hada masa duka hukuncin nan biyu.

Rufe ofishin NNPP a Borno

Mun ji labari cewa Gwamna Babagana Zulum da APC ba su da labarin ‘Yan Sanda da Jami’an Gwamnati sun rufe babban ofishin Jam’iyyar NNPP a Borno.

Kara karanta wannan

Bayan Samun Tikitin Jam’iyya, ‘Dan takaran APC zai Fuskanci Shari’a 19 Kafin 2023

NNPP tana zargin da hannun gwamna, amma Shugaban APC na Borno, Hon. Ali Bukar Dalori yace rikicin NNPP tsakanin jama'a ne da jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng