APC: Muna Ganin Girman Kwankwaso, Babu Hannunmu Wajen Garkame Ofishin NNPP

APC: Muna Ganin Girman Kwankwaso, Babu Hannunmu Wajen Garkame Ofishin NNPP

  • Shugaban APC na reshen jihar Borno ya maidawa jam’iyyar NNPP martani a kan zarginta da hannu wajen rufe mata ofis a Maiduguri
  • Hon. Ali Bukar Dalori ya fitar da jawabi yana mai cewa an rufe sakatariyar NNPP ne saboda BUDB tana zargin jam’iyyar da saba doka
  • APC mai mulki ta wanke Gwamna Babagana Zulum daga zargi, tace Mai girma Gwamnan bai bada umarni a taba hedikwatar NNPP ba

Borno – Jam’iyyar APC ta reshen jihar Borno, ta nesanta kanta daga zargin rufe wani gini da aka maida ya zama hedikwatar jam’iyyar NNPP a Maiduguri.

A wani jawabi da ya fito daga shugaban APC a Borno, Ali Bukar Dalori yace ba da hannunsu aka rufe ofishin NNPP ba, Vanguard ta kawo wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An Bude Sakatariyar NNPP A Jihar Borno, Zulum Ya Bamu Hakuri: Kakakin Kwankwaso

Hon. Ali Bukar Dalori yake cewa jam’iyyar APC tayi mamakin jin NNPP na zarginta ko Gwamnan Borno da bada umarnin garkame mata sakatariya a jiya.

Babu ruwan APC - Hon. Ali Bukar Dalori

“Hankalinmu ya zo ga wani zargi mara tushe da ake yi wa APC ta Borno da Mai girma Babagana Zulum na rufe sakatariyar NNPP a Maiduguri.”
“A matsayin shugaban kwamitin IPAC na duka jam’iyyun siyasar Najeriya, ina so in fada da babbar murna, APC tana daraja duka ‘yan siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musamman jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda tsohon ‘dan jam’iyyarmu ne, kafin ya zabi ya sauya sheka.”
Ofishin NNPP
Bikin bude ofishin NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Mazauna Abbaganaram ne suka kai kuka

Jawabin ya kara da cewa APC ba ta san labarin abin da ya wakana tsakanin NNPP da jami’an BUDB da ‘yan sanda da kuma mazauna Abbaganaram ba.

Kara karanta wannan

"Yadda Zulum Ya Umarci ‘Yan Sanda Su Garkame Sakatariyar NNPP a jihar Borno"

Rahoton yake cewa bincike ya nunawa Dolori cewa Babagana Zulum da jam’iyyar APC ba su san da batun ba, domin ko PDP ba a taba rufewa ofis ba.

Jagoran NNPP a Borno, Attom Magira Tom shi ne wanda ake zargi ya rikidar da wannan gini da yanzu yake aiki a matsayin ofis a Abbaganaram.

Mazauna unguwar da wannan ofishi yake na Abbaganaram sun koka a kan yadda su Hon. Attom Tom suka kafa sakatariyar siyasa a tsakiyar gidajensu.

Aikin Zulum ne - NNPP

Kun ji yadda kwamitin yakin neman takarar Rabiu Kwankwaso suka zargi Gwamna Babagana Umar Zulum da hannu a abin da ya auku a ranar Alhamis.

Jam’iyyar adawar tace an yi hakan ne saboda ziyarar da Rabiu Kwankwaso zai kawo.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdu Umar ya tura jami’an tsaro zuwa sakatariyar jam’iyyar adawar, yace sun samu korafi ne daga mazauna.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Fallasa Salon Dabarar Cin Zabenta da inda Kwankwaso Zai Fuskanci Cikas

Asali: Legit.ng

Online view pixel