Atiku Ya Shirya Zuwa Kano Domin Dauke Shekarau Daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP

Atiku Ya Shirya Zuwa Kano Domin Dauke Shekarau Daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP

  • Atiku Abubakar zai kawo ziyara zuwa Kano a ranar Lahadi, zai karbi Sanata Ibrahim Shekarau da magoya bayansa a PDP
  • Akwai alamun cewa Ibrahim Shekarau zai rungumi tafiyar Atiku Abubakar wanda shi ne Ɗan takarar shugaban kasa
  • Sanatan na jihar Kano ta tsakiya zai fice ne daga jam'iyyar hamayya ta NNPP duk da an ba shi takara ba tare da hamayya ba

Kano - Atiku Abubakar mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 zai ziyarci jihar Kano domin zawarcin Ibrahim Shekarau.

Kamar yadda muka samu labari daga BBC Hausa a ranar Asabar, Atiku Abubakar zai je jihar Kano domin karasa farautar magoya bayan Sardaunan Kano.

Wata majiya ta shaida cewa ‘dan takaran zai jawo tsohon gwamnan na Kano bayan an ji yana kukan cewa Rabi’u Kwankwaso ya yaudare su a NNPP.

Kara karanta wannan

Osinbajo, Lawan, Da Sauran Mutum 20 Da Suka Sayi Fom Din APC Zasu Gana Don Tinubu

Wannan taro da za ayi gobe zai zo gabanin sanarwar da Sanatan jihar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau zai bada na sake shiga jam’iyyar adawar.

Rahoton da muka samu daga Sahelian Times yace tsohon Gwamnan na Kano zai shiga kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a shekara mai zuwa.

Malam Shekarau yana cikin wadanda za su jagoranci takarar PDP a yankin Arewa maso yamma. Ana sa ran zai taimaka wajen yakar gwamnatin APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku
Atiku a jirgi Hoto: Mubailu Atiku Abubakar Support Group
Asali: Facebook

Daga Landan zuwa Kano

Idan abubuwa sun tafi yadda aka tsara, gobe jirgin Wazirin na Adamawa zai dura jihar Kano. Har zuwa ranar Juma’a, ‘dan takaran na PDP yana Ingila.

The Cable tace PDP za ta bar wa Shekarau takarar kujerar Sanatansa a zaben 2023. Baya ga haka, za a ba tsagin Shekarau mukamai idan ya bi tafiyar Atiku.

Kara karanta wannan

Magidanci Mai Mata 4 Da 'Yaya 34 Sun yi Rijistan Zabe, Yace Atiku Duk Zasu Kadawa Kuri'u

Tun tuni ake rade-radin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wa Shekarau alkawari masu tsoka, amma Sanatan ya musanya wadannan maganganu.

Shekarau a PDP

Ba wannan ne karon farko da Shekarau ya shiga PDP ba. Tsakanin 2014 da 2018 yana cikin jagororin jam’iyyar, a sakamakon ficewarsa daga APC mai mulki.

Daga baya Gwamna Abdullahi Ganduje ya kwadaito da Shekarau zuwa APC kafin zaben 2019, aka kuma ba shi takarar Sanata da yake kai har zuwa yau.

Zaman Atiku da Wike

Kwanan nan aka ji labari Alhaji Atiku Abubakar yace babu wani rikici tsakaninsa da Gwamnan Ribas watau Nyesom Wike a tafiyarsu ta jam’iyyar PDP.

Kamar yadda Atiku Abubakar ya fada a wani jawabi, maganar rikicin gidan PDP da ake yi, sharrin jam’iyyar APC mai mulki ne domin ta lashe zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng