Yadda Obasanjo Yake Kokarin Shawo Kan Wike, Ya Marawa Obi Baya Kan Atiku

Yadda Obasanjo Yake Kokarin Shawo Kan Wike, Ya Marawa Obi Baya Kan Atiku

  • Olusegun Obasanjo ya hadu da Gwamnan jihar Ribas watau Nyesom Wike ne saboda yana neman a marawa Peter Obi baya
  • Tsohon shugaban Najeriyan ya yi zama da Nyesom Wike a Landan a yunkurin tallata ‘dan takaran na LP a zaben shugaban kasa
  • Baya ga Obasanjo, tawagar Bola Tinubu da Atiku Abubakar duk sun zauna da Wike da nufin samun goyon bayansa a zaben 2023

London - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo yana goyon bayan Peter Obi ya karbi shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.

Rahoton da muka samu daga The Cable ya nuna cewa abin ya kai Olusegun Obasanjo ya nemi Nyesom Wike ya marawa takarar Peter Obi baya.

Saboda ya nemi kamun kafa, Obasanjo wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007 ya bukaci ya zauna da Gwamnan na jihar Ribas a birnin Landan.

Kara karanta wannan

Atiku ya kade: Obasanjo ya gana da Peter Obi, Wike da wasu jiga-jigai a Landan

Majiyar tace Cif Obasanjo yana ganin bai kamata mulki ya koma Arewa ba, don haka bai goyon bayan irinsu Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2023.

Mulki ya bar Arewa a 2023

“Obasanjo yana son mutumin kudu ya zama shugaban kasa, amma bai tunanin cewa Bola Tinubu ne wanda yafi dacewa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tsohon shugaban kasar Najeriya ya roki Gwamna Nyesom Wike da kuma magoya bayansa su mara baya ga Peter Obi.”

- Majiya

Obasanjo, Obi da Wike
Obasanjo, Obi wasu Gwamnoni da Wike Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahoton bai bayyana ko Mai girma Wike ya amsa wannan bukata ta Olusegun Obasanjo ba. Har yanzu ba a san ina Gwamnan ya dosa ba.

Wa Wike zai marawa bata?

A ‘yan kwanakin bayan nan, ‘dan takaran na jam’iyyar LP watau Peter Obi ya hadu da Gwamna Wike akalla sau uku a garin Fatakwal da kasar waje.

Kara karanta wannan

“Atiku Abubakar Zai Doke Bola Tinubu a Legas a Zaben Shugaban Kasan 2023”

Amma dai a lokacin da Obasanjo da su Peter Obi su ka yi zama da Gwamnan na Ribas ne kuma sai ga shi ya sa labule da tawagarsu Atiku Abubakar.

‘Dan takaran shugaban kasar na PDP ya ci abinci da abokin hamayyarsa a zaben tsaida gwani da aka yi, a yanzu yana neman goyon bayansa.

A makon nan ne dai Bola Tinubu da wasu gwamnonin APC suka yi zama da Wike da ‘yan bangarensa, da nufin ya taimaka masu a zabe mai zuwa.

Babu sabani a PDP

An ji labari an yi wata haduwa a Ingila domin dinke barakar da ake tunanin ana samu tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike a tafiyar PDP.

‘Dan takaran shugaban kasar ya gargadi mutanensa da su yi hattara da wata baram-baramar da za ta iya jawo a fadi zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel