"Yadda Zulum Ya Umarci ‘Yan Sanda Su Garkame Sakatariyar NNPP a jihar Borno"
- A yau ne aka samu labari jami’an tsaro sun ziyarci hedikwatar jam’iyyar hamayya ta NNPP na jihar Borno, sun garkame ofishin
- Kwamitin yakin neman takarar Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Gwamna Babagana Zulum da hannu a abin da ya auku
- A wani jawabi da ya fito daga ofishin Muyiwa Fatosa, jam’iyyar adawar tace an yi hakan ne saboda ziyarar Rabiu Kwankwaso
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Kwamitin yakin neman takarar Rabiu Musa Kwankwaso a zaben shugaban kasa, ya yi magana a kan rufe ofishin NNPP da aka yi a jihar Borno.
Kwamitin neman zaben ya fitar da jawabi na musamman da aka yi wa take da ‘Rufe hedikwatar jam’iyyar NNPP a Maiduguri da gwamnatin Borno tayi.’
Kamar yadda Daily Nigerian ta fitar da wannan labari, Muyiwa Fatosa ya sa hannu a jawabin dazu.
Muyiwa Fatosa ya bayyana cewa baya ga garkame babban ofishin jam’iyyar ta NNPP na reshen jihar Borno, an bugi ma’aikata, sannan an lalata kayan aiki.
Zargin da kwamitin yakin neman zaben Rabiu Musa Kwankwaso na zama shugaban kasa yake yi shi ne Gwamna Babagana Zulum ya bada umarnin hakan.
Ana zargin Mai girma Farfesa Zulum da yin wannan saboda jin labarin Rabiu Kwankwaso zai kawo ziyara garin Maiduguri a ranar Asabar mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Hakan na zuwa ne a lokacin da jagoran NNPP na kasa, ‘dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, PhD FNSE zai ziyarci Borno domin kaddamar da ofishin nan da kwanaki biyu, a ranar 27 ga watan Agusta, 2022.
“Idan za a tuna, Kwankwaso yana zagaye kasar nan wajen bude ofisoshin NNPP, inda yake samun karbuwa sosai daga magoya baya cikin kwanciyar hankali, ba za a bar Borno a gefe ba.”
- Muyiwa Fatosa
Jawabin na Fatosa ya yi tir da wannan danyen aiki da jami’an tsaro suka yi, yace hakan na nuna irin mummunan abin da zai faru a zabe mai zuwa.
Jaridar tace Mista Fatosa ya yi kira ga gwamnatin Borno ta bude sakatariyar, a kuma bada umarni ga jami’an tsaron da ke wurin, su kama hanyar gabansu.
'Dan takaran Gwamna ya koka
Dr. Umar Alkali ya shaidawa manema labarai abin da ya faru a yau, yace wannan barazana ba za ta kawowa ‘dan takararsu, Rabiu Kwankwaso cikas ba.
A wani bidiyo da aka fitar a Twitter, an ji Umar Alkali yace yanzu haka 'dan takaran Sanatan Borno ta tsakiya a jam'iyyar NNPP yana hannun 'yan sanda.
NNPP ta shiga ko ina
An ji cewa shugaban Jam’iyya mai kayan marmari, Farfesa Rufa’i Alkali yace NNPP ba karamar jam’iyya ba ce, a daina yi mata kallon ba za ta je ko ina ba.
Farfesan yace a yau duk Najeriya, babu jam’iyyar siyasar da ta fi NNPP saurin yaduwa, yace da zarar an soma kamfe, za a ga irin karfin da jam'iyyar tayi.
Asali: Legit.ng