NNPP Ta Fallasa Salon Dabarar Cin Zabenta da inda Kwankwaso Zai Fuskanci Cikas

NNPP Ta Fallasa Salon Dabarar Cin Zabenta da inda Kwankwaso Zai Fuskanci Cikas

  • Farfesa Rufa’i Alkali ya bayyana cewa ba daidai ba ne a rika tunani NNPP ba ta da karfin da za ta iya lashe zaben shugabancin Najeriya
  • Shugaban jam’iyyar ta NNPP ta kasa yace duk Najeriya babu jam’iyyar da ke samun karbuwa sosai a yanzu irin NNPP mai kayan dadi
  • Rufa’i Alkali yake cewa sun fara ratsa duk wani lungu da kwaroro da ke kasar nan da nufin ganin jam’iyyar hamayyar tayi nasara a badi

Abuja - Shugaban NNPP na kasa, Farfesa Rufa’i Alkali ya yi raddi ga masu cewa jam’iyyarsu ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa mai zuwa ba.

Farfesa Rufa’i Alkali ya bayyana wannan ne a lokacin da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN tayi hira da shi a ranar Laraba a garin Legas.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Tsohon sakataren yada labaran na PDP yake cewa wasu suna tunanin babu inda NNPP ta ke da karbi illa a jihar Kano, yace ba haka abin yake ba.

A cewar Farfesa Alkali, a ‘yann watanni hudu da suka wuce, jam’iyyar ta shiga sauran lungu da kwararon Najeriya domin ganin ta lashe zabe.

NNPP za ta bada mamaki a 2023?

Daily Nigerian ta rahoto shugaban jam’iyyar adawar yana mai cewa kuskure ne a rika tunanin ba za su kai labari ba, yace sun shiryawa zaben badi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, NNPP tana ratsa jihohi, tana jawo jama’a, kuma ta tsaida ‘yan takara a zaben gwamnonin jihohi da majalisun jihohi da kuma tarayya.

'Dan takaran NNPP
'Dan takaran NNPP, Kwankwaso a jihar Bauchi Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A hankali ake farawa - Alkali

“Duk wata jam’iyyar siyasa a Najeriya da Afrika ta na farawa ne sannu a hankali. Babu jam’iyyar da ta gawurta rana daya.

Kara karanta wannan

Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

Kowace jam’iyyar siyasa tana da kalubalenta na cikin gida, amma mu ba jam’iyyar da za a ce rikicin gida ya dabaibaye ta ba ne.
NNPP ba karamar jam’iyya ba ce, kai ita ce jam’iyyar siyasar da ta fi kowace saurin yaduwa a kasar nan, mun shiga ko ina.

Kalubale a zaben 2023

The Cable ta rahoto Farfesan ilmin siyasa da tattalin arzikin yana mai cewa jam’iyyar tana kokarin shawo kan rigingimun da suka bijiro mata.

Alkali yace an kafa kwamitocin sulhu a matakai na kasa, shiyyoyi da jihohi domin a dinke duk wasu baraka, yace idan an fara kamfe, za a ga karfinsu.

A hirar da aka yi da shi, Farfesan ya yarda NNPP ba ta da karfi a kasar Kudu maso gabas, yace ana kokarin ratsa yankin, sai dai PDP ta karbe yankin.

Rikicin gidan PDP

An ji labari jam’iyyar PDP da ‘Dan takaranta sun gaji da jiran lokacin da za a sasanta da Gwamna Nyesom Wike, za a kafa kwamitocin yakin takaran 2023.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ayu Yayi Martani Kan Zarginsa da Wike Yayi na Cin Rashawar N100m da N1b

A lokacin zaben 2019, Bukola Saraki ne ya zama Shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, jama’a za su zura ido domin ganin kwamitin bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel