“Atiku Abubakar Zai Doke Bola Tinubu a Legas a Zaben Shugaban Kasan 2023”

“Atiku Abubakar Zai Doke Bola Tinubu a Legas a Zaben Shugaban Kasan 2023”

  • Sanata Dino Melaye yana ganin jam’iyyar PDP za ta shiga har Legas, ta koyawa Asiwaju Bola Tinubu darasi a siyasar 2023
  • Melaye wanda shi ne Mai magana da yawun kwamitin takarar Atiku Abubakar yace ‘dan takaran ya samu karbuwa a jihar
  • Ganin yadda ‘Dan takaran Gwamnan da PDP ta tsaida ya kifar da Gwamna a jihar Osun, Melaye ya hangowa PDP wata nasara

Abuja - Mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Dino Melaye yace mai gidansa zai doke APC a jihar Legas.

Daily Trust tace Sanata Dino Melaye ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi wata tattaunawa da shi a gidan talabijin na Trust TV a makon nan.

Domin nuna irin galabar da ‘dan takaran PDP zai yi a zaben shugaban kasa mai zuwa, Dino Melaye yace zai doke Asiwaju Bola Tinubu ko a gidansa.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Asiwaju Bola Tinubu ya yi gwamna a jihar Legas tsakanin 1999 da 2007, kafin nan ya yi Sanata a 19992, kuma har yau ana zargin yana da ta-cewa.

Zaben Osun ya isa aya - Dino

Da aka zanta da Melaye, kakakin kwamitin yakin neman zaben na Atiku Abubakar ya bada misali da yadda jam’iyyar APC ta sha kashi a jihar Osun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Melaye yake cewa asalin Bola Tinubu mutumin Osun ne, amma wannan bai hana ‘dan takaran PDP lashe zaben gwamna da aka yi a Yuli ba.

Atiku Abubakar
Atiku a wajen liyafa Hoto: Atikuorg
Asali: Twitter

Bugu da kari, Melaye yace Tinubu tamkar uba yake a wajen Gwamna mai-ci da aka doke a Osun.

Abin da ya sa PDP za ta ci zabe

“Idan aka shirya zabe yau a Legas, jama’iyyar PDP za ta lashe zaben, Atiku Abubakar zai doke Asiwaju Bola Tinubu.”

Kara karanta wannan

Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

“Atiku ya je Legas kwanaki biyu da suka wuce, kuma an tarbe shi duk inda ya je. Mutane na kaunarsa, zai lashe zabe.”

- Dino Melaye

Baya ga haka, an rahoto tsohon Sanatan yana cewa rikicin Atiku da tsagin Gwamna Nyesom Wike ba zai hana ‘dan takaran shugaban kasar cin nasara ba.

Babu adalci a PDP - Sanata Jibrin

An ji labari Walid Jibrin wanda shi ne shugaban majalisar BoT kuma da su ne aka kafa jam’iyyar a 1998, ya fito yana cewa an dannke 'Yan kudu a PDP

Yanzu maganar da ake yi a PDP, Shugaban jam’iyya na kasa, da Shugaban majalisar BoT da ‘dan takaran shugaban kasa duk 'Yan yankin Arewa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng