INEC Ta Kwantar da Hankalin Jama'a, Tace Murde Zaben 2023 Ba Zai Yiwu Ba

INEC Ta Kwantar da Hankalin Jama'a, Tace Murde Zaben 2023 Ba Zai Yiwu Ba

  • Kwamitin National Peace Committee (NPC) da cibiyar The Kukah Centre sun shirya taro a Abuja a shirin zaben 2023
  • Makasudin taron nan shi ne yadda za a karawa juna sani a yakar labaran bogi, kuma a taso ‘yan takaran siyasa a gaba
  • Farfesa Mohammad Kuna ya tabbatar da cewa ba za a iya murde sakamakon zabe ba saboda an shigo da na’urorin BVAS

Abuja - Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta tabbatarwa mutanen Najeriya cewa ba za ta yiwu ayi cuwa-cuwa wajen tattara sakamakon zabe ba.

Daily Trust tace Farfesa Mohammad Kuna ya bayyana haka a wajen wani taro da Kwamitin NPC da cibiyar The Kukah Centre suka shirya a Abuja.

Janar Abdulsalami Abubakar shi ne shugaban wannan kwamiti na NPC mai kawo zaman lafiya, sai Bishof Mathew Kukah yake jagorantar cibiyar.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

An yi wannan taro na karawa juna sani a ranar Talata, inda aka tattauna a kan irin gudumuwar da fasahar zamani za su bada wajen gudanar da zabe.

Shigowar na'urar BVAS

Farfesa Mohammad Kuna wanda Mai bada shawara na musamman ne ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yace fasahar BVAS za ta taimaka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Mohammad Kuna, da zarar malaman zabe suka yi amfani da wannan na’ura suka aika sakamakon kuri’un da aka kada a rumfa, magana ta kare.

INEC.
Shugaban INEC na kasa Hoto: inecnews.com
Asali: UGC

Na’urar BVAS da aka zo da ita tana amfani wajen tantance katin zabe da kuma mai kada kuri’a. BVAS ba za ta bari wani ya kada kuri'a da katin wani ba.

“Saboda yanayin BVAS, ba za ta yiwu a murde sakamakon zabuka rumfunan zabe da aka daura, ba a tsara na’urar ta taba kuri’un da aka aika IReV ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa

“Da zarar an tura da sakamakon zabe shikenan, ba za a iya dawo da shi ba.

- Farfesa Mohammad Kuna

Sauya jami'an zabe

Rahoton yace Kuna ya kuma yi karin-haske kan surutun da ake yi saboda an canzawa Injiniya Chidi Nwafor wurin aiki daga hedikwata zuwa Enugu.

Mai ba shugaban na INEC shawara na musamman yace hukumar zaben ta saba yin irin wannan sauye-sauye, hakan ya faru gabanin zaben 2011 da 2019.

Rikicin jam'iyyar PDP

An ji labari cewa Sanata Walid Jibrin ya fitar da jawabi a game da kokarin da aka yi na kawo karshen rigimar cikin gidan da ta kunno kai a jam’iyyar PDP

Walid Jibrin wanda shi ne Shugaban majalisar BoT ta PDP yana da ra’ayin cewa mutanen Arewa sun karbe manyan mukaman jam’iyyar hamayyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng