Buhari: Abin Da Yasa Ba Za Mu Iya Kara Wa Ma'aikata Albashi Ba Duk Da Ya Kamata

Buhari: Abin Da Yasa Ba Za Mu Iya Kara Wa Ma'aikata Albashi Ba Duk Da Ya Kamata

  • Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta san ya kamata a yi wa ma'aikata karin albashi amma akawai dalilin da suka hana
  • Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta iya karin albashin ba a yanzu saboda ta shafe shekaru bakwai tana kashe makuden kudi a bangaren tsaro
  • Shugaban ya kuma ce ana fama da karancin kudi a kasar saboda satar danyen mai da karyewar tattalin arzikin duniya saboda yakin Rasha da Ukraine da annobar korona

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a ya bada dalilin da yasa gwamnatin tarayya ba za ta iya yi wa ma'aikata karin albashi ba duk da ya kamata, The Punch ta rahoto.

Sanarwar da hadimin shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, ta ambaci Buhari na bada dalilai lokacin da kwamitin ayyuka na kungiyar manyan ma'aikatan Najeriya ta kai ziyara a gidan gwamnati a Abuja.

Kara karanta wannan

'Zan Fitar Da Najeriya Daga Duhu', Atiku Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Bangaren Lantarki

Shugaba Buhatri
Buhari: Abin Da Yasa Ba Za Mu Iya Kara Wa Ma'aikata Albashi Ba Duk Da Ya Kamata. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Depositphotos

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wa sanarwar take da 'Rahoton Oronsaye za ta haifar da canji a ayyukan gwamnati, Buhari ya bada tabbaci".

Martanin Buhari kan bukatar kwamitin na karin albashi

Shugaba Buhari, yayin martani kan bukatar yi wa ma'aikatan karin albashi ya ce duk da cewa ana bukatar karin sosai saboda hauhawar farashin kayayaki na duniya, gwamnati na fama da karancin kudin shiga da kallubalen tsaro a kasar ya janyo.

Ya ce:

"Ina son ku yi la'akari da karancin kudin shiga da gwamnati ke fuskanta, wanda satar danyen mai da wasu bata gari ke yi ya janyo, kasancewar mai ne babban hanyar kudin shigar mu.
"Hakazalika, karyewar tattalin arziki a duniya sakamakon yakin Rasha da Ukrain, ya janyo karin farashin kaya da ayyuka a duniya da ma kudin jigilar kaya da ayyuka.

Kara karanta wannan

Buhari ga jami'ai: Ku tabbata kun kawar 'yan ta'addan Najeriya gaba daya

"Kun kuma san matsalar da tattalin arzikin mu ta shiga saboda COVID-19. Kuma mun kashe kudade sosai a bangaren tsaro cikin shekaru bakwai da suka shude, hakan na nufin wasu sassan tattalin arzikin ba su samu kudin muka so mu ware musu ba. Don sai da tsaro sannan za mu iya bada karfi a sauran bangarorin tattalin arziki."

Buharin ya bada umurnin a yi nazarin shawarwarin da ke cikin takardar ta rahoton Orosanye don gwamnati ta aiwatar da shawarwarin.

Ya ce an kusa gama nazarin kuma idan an kama, abubuwan da za a aiwatar za su kawo manyan canje-canje masu amfani a aikin gwamnati.

Cikakken Albashi Da Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa Da Na Gwamnoni Da Mataimakansu Ya Bayyana

Batun albashin zababbun shugabanni a Najeriya lamari ne da ya dade yan Najeriya suna tafka muhawara a kansa.

Yayin da yan Najeriya ke ganin albashin da yan siyasan ke karba ya yi yawa, yan siyasan kuma a bangarensu su kan kare kansu ta hanyar bada dalilan da yasa suke karbar irin wannan albashin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ya kamata daliban jami'a su maka ASUU a kotu, su nemi diyyar bata lokaci

Wata takarda da aka wallafa a shafin intanet na RMAFC ya nuna albashi da allawus din shugaban kasa, mataimakinsa da wasu tun daga Fabrairun 2007 zuwa Yunin 2009.

Asali: Legit.ng

Online view pixel