Na Bar Koyarwa Har Abada Idan Aka Hana Mu Albashin Watanni 6 Inji Malamin Jami’a

Na Bar Koyarwa Har Abada Idan Aka Hana Mu Albashin Watanni 6 Inji Malamin Jami’a

  • Dr. Auwal Mustapha Imam ya koka a kan irin kulawar da gwamnatin tarayya ta ke ba malaman jami’o’i duk da baiwar ilmin zamaninsu
  • Wannan masani wanda ya karanci ilmin lantarki a Najeriya da kasar waje yace ba zai cigaba da koyarwa ba idan aka hana su albashinsu
  • Abin da ya tunzura Auwal Mustapha Imam shi ne ganin mawakin nan, Rarara ya shiga jirgin sojoji a lokacin da malaman jami’a ke hamma

Kaduna – Dr. Auwal Mustapha Imam, wani malamin jami’a a Najeriya, ya fito yana matukar nuna Allah wadai da halin da ilmi ya shiga a yau.

Da yake bayani a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, Dr. Auwal Mustapha Imam ya koka a kan yadda sam ba a girmama malamai a kasar nan.

Malamin yake cewa tabbas zai daina koyarwa idan har gwamnatin tarayya ba za ta biya su albashin watannin shida da suka yi wajen yajin-aiki ba.

Kara karanta wannan

Daliban Jami’a Sun Ki Daukar Shawarar Minista, Za Su Kai Gwamnati kotu kan ASUU

A cewar Auwal Imam wanda ya yi karatu a kasar Malaysia, duk Arewacin Najeriya shi kadai ne ya kware a fannin da ya samu shaidar digirdigir.

Malamai sun zauna babu albashi

Ganin ana fama da karancin malamai a mahaifarsa, yace shi ya sa ya dawo gida domin ya bada gudumuwarsa, duk ya samu dama a kasar waje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun watan Fubrairu aka rufe jami’o’i saboda yajin-aikin ASUU, hakan ya sa gwamnatin Muhammadu Buhari ta daina biyan malamai albashi.

Dauda Kahutu Rarara
Dauda Kahutu Rarara sun fito daga jirgi Hoto: Aliyu Samba
Asali: Facebook

Kamar yadda ya fada a Facebook, Auwal Imam yace kungiyar ASUU ta shiga yajin-aiki ne domin gyara a harkar ilmi, sai ga shi ana yi masu barazana.

Malamin ya na mai zargin gwamnatin tarayya da kin cika alkawaran da ta yi wa kungiyar ASUU.

Rarara a jirgin sojoji

Auwal Mustapha Imam ya yi wannan magana ne bayan ganin shahararren mawakin nan watau Dauda Kahutu Rarara a kusa da jirgin sojoji.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ya kamata daliban jami'a su maka ASUU a kotu, su nemi diyyar bata lokaci

Masanin yace duk da mawakin bai amfanar Najeriya da komai, sai ga shi ana yawo da shi a jirgin saman gwamnati, yayin da malamai ke shan wahala.

Legit.ng Hausa ta fahimci an ragewa Sha’aban Sharada da Rarara hanya ne a lokacin da hafsun sojojin sama zai iyarci Kano, akasin yadda wasu ke fada.

Bayan nan sai wannan Bawan Allah yake ta ishara ga wasu malaman jami’o’i da ke nuna za su ajiye aikinsu, su na nuna sun gaji da aiki da gwamnati.

Me Dr. Auwal Mustapha Imam ya fada?

"PhD ne da ni. Duk Arewa ni kaɗai na ƙware a arean da na ƙware. Ina koyarwa a jami'o'i guda biyu na gwamnatin tarayya. Wasu jami'a'o'in na buƙatar aiki na. Muna da damar aiki mai kyau a ƙasashe da yawa da ake mutunta ilimi, amma muka zaɓi mu dawo gida saboda babu isassun Malamai. Ana biyanmu abinda ba ya iya ɗaukar nauyin hidindimunmu.

Kara karanta wannan

Ba Za a Bude Jami’o’i Kwanan nan ba, ASUU Tayi Magana Kan Dogon Yajin-Aikinta

Gwamnati ta yi alƙawura na inganta rayuwarmu, amma an gaza. Mun shiga yajin aiki domin nema wa kawunanmu mafita, amma gwamnati na barazanar ƙin biyanmu albashinmu da aka riƙe na wata shida.
Ga wannan mawaƙin waƙa kawai ya iya, ba ya amfanar da Nigeria to kowace hanya. Amma a jirgin ƙasar mu ake ɗaukar sa. Mu kuma da muke bauta wa ƙasar mu, mun zama abin wulakantawa.
Na rantse da Allah! Idan gwamnati ba ta biyamu albashinmu na wata shida ba, na bar aikin jami'a kenan har abada!"

- Dr. Auwal Mustapha Imam

An hana ni shiga takara

Kwanaki kun ji labari Auwal Mustapha Imam wanda ya nemi takarar shugabancin karamar hukumar Zaria yana cewa an yi masa ba daidai ba APC.

Malamin makarantar ya koka da hana shi takara da jam'iyyar APC tayi. Imam mai digirin PhD, ya zargi kwamitin tantance 'yan takara da yi masa sharri.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi Sun Ji Zafi, Sun Kai Karar El-Rufai Wajen Kamfanin Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng