Tantance 'yan takarar LG na APC: Mai digirin digirgir ya koka kan hana shi takara

Tantance 'yan takarar LG na APC: Mai digirin digirgir ya koka kan hana shi takara

- Dan takarar shugabancin karamar hukumar Zaria, Dakta Auwal Mustapha Imam ya koka da hana shi takara da APC tayi

- Imam mai digirin digirgir, ya zargi kwamitin tantance 'yan takara da yin batanci garesa inda suka ce baya biyayya ga jam'iyyar APC

- Kamar yadda ya bayyana, ya zargi kwamitin da cire shaidar digirinsa na 3 duk da ya mika musu, domin su nuna wani ya fi shi cancanta

Mai digirin digirgir, Dr Auwal Mustapha Imam, wanda kwamitin tantancewa na jam'iyyar APC a jihar Kaduna suka hana takarar kujerar shugabancin karamar hukuma, ya koka akan abinda ya faru.

Imam yana daya daga cikin daruruwan 'yan takarar da aka sa suka rubuta jarabawa tare da tantancesu karkashin kwamitin tantancewa kafin zuwan zaben fidda gwani a jihar Kaduna.

Kamar yadda ya sanar da Legit.ng, "Kwamitin tantance ƴan takara sun yi batanci gareni ta hanyar lakaba min cewa ba na biyayya ga jam'iyya."

KU KARANTA: Yahaya Bello: Buhari na kaunar matasan Najeriya, yana basu dama masu yawa

Jarabawar 'yan takarar LG na APC: Mai digirin digirgir ya koka kan hana shi takara
Jarabawar 'yan takarar LG na APC: Mai digirin digirgir ya koka kan hana shi takara
Asali: Original

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Rundunar 'yan sandan Legas ta bada umarnin cafke mutum 13

Dakta ya yi korafin cewa an yi hakan ne domin cin mutuncinsa da kuma bata masa suna. Domin shi Uba ne, Malami kuma jagora ne ga al'umma da yawa.

Ya yi zargin cewa ya bayar da takardunsa na makaranta lokacin cike form ɗin takara da kuma lokacin tantancewa, amma abin mamaki sai aka cire babbar takardar karatunsa na digiri na uku (PhD), domin ana so a nuna wani dan takara da matakin karatunsa bai je ko ina ba ya yi nasara a kansa.

Amma a cewar Dakta, shi mai biyayya ne ga jam'iyya tun lokacin da ya shige ta, haka ne yasa ya shigar da korafi ta hannun lauyoyinsa ga kwamitin da aka nada domin ɗaukaka koken ƴan takara.

Ya ce yana sauraron sakamakon ɗaukaka koken, kuma yana kira ga kwamitin da kuma jam'iyya da su janye kalaman batanci da aka yi a gareshi, sannan su wanke sunansa.

Dakta Auwal dai na cikin na gaba-gaba a ƴan takaran kujerar shugabancin ƙaramar hukumar Zaria wurin soyuwa a wurin jama'a. Ya shiga lungu da sako daban-daban domin yakin neman zabe. Wasu na ganin yi masa wannan batanci ba zai rasa nasaba da nasarorin da yake samu ba wurin soyuwa a wurin jama'a.

A nasa cewar, "Idan har siyasar ake da gaske, kamata ya yi a buga da ni a fagen daga ba wai a yi amfani da hanyoyin da basu dace ba wurin cire ni daga takara ba."

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna tace dakarun sojin Najeriya sun halaka wata kungiyar 'yan bindiga dake jihar.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma'a, yace 'yan bindigan sun tattaru ne domin kaddamar da wani hari a karamar hukumar Birnin Gwari.

Kamar yadda yace, dakarun sojin saman rundunar Operation Thunder Strike sun fada aiki kuma sun kawar da 'yan bindigan a yankin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel