Ni Na San Matsalar Tsaron Najeriya, Kuma Ni Zan Iya Magance Ta, Inji Kwankwaso
- Dan takarar shugaban kasan NNPP ya bayyana kwarin gwiwarsa ta gyara Najeriya idan aka ba shi ragamarta
- Kwankwaso ya tuna cewa, shi tsohon ministan tsaro ne, don haka gyara tsaron Najeriya abu ne mai sauki a gare shi
- Kwankwaso ya sha bayyana aniyarsa ta hade kan 'yan Najeriya tare da kawo sauyi mai kyau a kasar
Lafia, Nasarawa - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya magantu kan batun da ya shafi tsaron Najeriya, ya kuma bayyana cewa shi dai ya san mafita.
Kwankwaso, wanda shi ne mai jan ragamar jam'iyyar NNPP kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023 ya zai iya magance matsalar tsaron Najeriya idan 'yan Najeriya sun ba shi dama.
Ya ce ya lura cewa, Najeriya na da matsaloli, kuma babu matsalar da ta kai ta tsaro girma a kasar.
Da yake karin haske tare da bayyana kwarin gwiwarsa, ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“A matsayina na tsohon ministan tsaro, ina da matukar sani game da harkar tsaro. Ina da yakinin cewa sojojinmu na da karfin dakile wannan matsala ta hanyar siyasa, karin gwiwa, horo da karin horo ga jami'ai."
Hakazalika, ya yi tsokaci game da matsalar tattalin arziki, inda nan ma yace ba zai yi kasa a gwiwa ba, zai tabbatar da abubuwan sun inganta saboda irin abubuwan da zai mai da hankali a kai kenan.
Jaridar Daily Nigerian ta ce Kwankwaso ya bayyana hakan ne ga manema labarai a birnin Lafia a yau Lahadi 21 ga watan Agusta.
Game da batun cin hanci da rashawa, Kwankwaso ya ce nan ma ba zai bari mahandama su rike wurare su yi kememe ba, dole zai yaki cin hanci da rashawa a Najeriya.
Da yake tabi bangaren hakar ma'adinai, Kwankwaso ya ce zai tabbatar da ana yin sana'ar cikin tsari da kuma yardar gwamnatin, musamman a jihar Nasarawa.
Manufa ta hade kan 'yan Najeriya, inji Kwankwaso
Ya kuma gargadi masoyansa da 'yan a mutun NNPP da su guji kalaman batanci, inda ya sake jaddada aniyarsa ta hada kan 'yan Najeriya baki daya.
A bangare guda, ya shawarci 'yan Najeriya da su darje wajen zaben shugabanni a 2023 domin kaucewa zaben tumun dare.
Ba wannan ne karon farko da Kwankwaso ke fadin irin wadannan maganganu na daidaita Najeriya idan ya gaji kujerar Buhari, ya fadi irin wannan magana a Calabar a watan Yunin da ta gabata, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Tawagar Gwamna Wike da Ta Atiku Sun Shigawa Ganawar Sirri Don Neman Sulhu
A wani labarin, daga karshe dai sashen gwamnan Ribas Nyesom Wike da na dan takarar shugaban kasan jam’iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar sun gana a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas domin dinke baraka.
A cewar rahoton jaridar The Nation, ganawar ta samu halartar gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a matsayin jagoran tawagar Atiku da, inda suka dira fadar gwamna Wike a madadin Atiku.
Tun bayan kammala zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na dan takarar shugaban kasa Wike da Atiku ke zaman doya da manja saboda wasu mabambantan ra'ayoyi da ke tsakani.
Asali: Legit.ng