Za Ka Iya Shan Kaye A Zaben 2023, Wike Ya Fada Wa Atiku

Za Ka Iya Shan Kaye A Zaben 2023, Wike Ya Fada Wa Atiku

  • Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya gargadi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar cewa zai iya shan kaye a zaben
  • Wike ya fada wa Atiku cewa mutanen da ke zagaye da shi galibinsu surutu kawai suke a soshiyal midiya a maimakon su mayar da hankali kan yadda za a ci zaben
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya shawarci Atiku ya umurci mutanen da ke tare da shi a Abuja su koma garuruwansu su fara yi masa kamfen domin ta haka ne zai yi nasara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya fada wa Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya yi takatsantsan da mutanen da ke zagaye da shi idan yana son cin zaben shekarar 2023, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Abin Da Zan Yi Bayan Na Lashe Zaben Shugaban Kasar Najeriya A 2023

Wike Nyesom
Za Ka Iya Shan Kaye A Zaben 2023, Wike Ya Fada Wa Atiku. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Da ya ke magana a Port Harcourt wurin taron kaddamar da Gidajen yan majalisar dokokin jihar Rivers da Kakakin Majalisar Wakilai na tarayya, Femi Gbajabiamila ya yi a ranar Juma'a, Wike ya ce wadanda ke zagaye da Atiku za su iya sa ya fadi zabe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike ya ce wasu mutane suna can suna neman ganin bayansa a maimakon su mayar da hankali kan yadda za su ga PDP ta ci babban zaben da ke tafe, Information Nigeria ta rahoto.

"Abin da ya kamata dukkan masu son PDP ta ci zabe su mayar da hankali kai. Ya kamata ku rika maganan yadda za ku ci zabe. Dukkan wadanda masu neman fada a wurin shi (Atiku) bai taimaka masa suke ba. A maimakon hakan suna kokarin ganin bai ci zabe ba. Amma idan haka suke so, ina musu fatan alheri."

Kara karanta wannan

Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, Ana yi wa Addininsa Barazana

"Ka ga ba maganganu na tsaya yi ba. Ina aiki na, don haka ku kyale ni in yi aiki na. Wadanda ke kirkirar maganganu kullum, soshiyal midiya ba zai sa ka ci zabe ba. Zabe batu ne na mutane don mutane. Wadanda ke tare da kai (Atiku) a Abuja, ka fada musu su koma gida su maka kamfen don ka ci zabe. A kyalle Wike, abin ya isa haka," in ji shi.

Wike ya kuma nesanta kansa daga wadanda suka shigar da kara a kotu na neman a cire sunan Atiku daga jerin yan takarar shugaban kasa na zaben shekarar 2023.

Wike Ya Yi Magana Kan Karar Da Aka Shigar Na Neman Tsige Atiku A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

Gwamna Wike ya nesanta kansa daga ƙarar da aka rahoto cewa an shigar a kotu na neman soke Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, kamar yadda ThisDay ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

Magoya bayan Wike sun kai Atiku da Aminu Tambuwal, gwamnan Jihar Sokoto da hukumar INEC kotu kan yadda aka yi zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP da aka yi a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel