Tashin Hankali a APC Yayin da Jam’iyyar Ta Gaza Mayarwa ’Yan Takarar da Suka Janye Kudin Fom

Tashin Hankali a APC Yayin da Jam’iyyar Ta Gaza Mayarwa ’Yan Takarar da Suka Janye Kudin Fom

  • Jam'iyyar APC ta gudanar taronta na gangami a watan Maris, amma an samu tasgaro game da wasu alkawura da aka dauka
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci APC ta mayarwa 'yan takarar shugabancin APC a taron kudadensu na sayen fom
  • Jam'iyyar APC ta rikide wajen gaza biyan albashin mambobi da masu ruwa da tsaki a kan, kana ana bin jam'iyyar albashin wasu watanni

FCT, Abuja - Watanni hudu bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a mayar wa ‘yan takarar da suka janye daga takarar APC a taron gangami na ranar 26 ga Maris, har yanzu jam’iyyar ba ta bi umarninsa ba.

Bincike ya kuma nuna cewa ‘yan majalisar da suka gudanar da taron na kasa (daga unguwanni zuwa matakin kasa) na bin APC kudade gabanin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

Jam’iyyar, a cikin watanni biyun da suka gabata, ta kuma gaza wajen biyan albashin ma’aikata kamar yadda ya kamata.

Yadda ake kai ruwa rana a APC saboda gaza mayar da kudin fom din takara
Tashin hankali a APC yayin jam'iyyar ta gaza mayar wa 'yan takarar da suka fadi kudin fom | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Rahoton The Nation ya ce APC ta biya albashin watan Yuni ne a tsakiyar watan Yuli kana ma’aikata suka ga alat na albashin watan Yuli a ranar Juma’ar da ta gabata, sabanin ranar 25 ga kowane wata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda batun ya faro daga fadar Buhari

A ranar 24 ga watan Maris ne shugaba Buhari ya gana da wasu ’yan takara a taron guda takwas, inda ya lallabe su da su janye daga takara domin samar da dan takarar yarjejeniya, tare da mayar musu da kudaden sayen foma-fomansu.

Kowane dan takara a jam’iyyar ya biya tsakanin N20m zuwa N2.5m domin nuna sha'awar tsayawa takara; ya danganta da ofishin takara.

Bincike ya nuna cewa jam’iyyar ta samu sama da N700m daga cikin mutane kusan 170 da suka fito takarar shugabancin jam'iyyar a matakai daban-daban..

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

An kuma bayyana cewa jam’iyyar ta samu sama da Naira biliyan 3 daga hannun mambobinta da suka sayi fom din nuna sha’awa da tsayawa takara a zabukan 2023 da ke tafe.

Sai dai duk da dimbin kudaden da aka samu, ‘yan jam’iyyar da abin ya shafa na korafin rashin bin umarnin shugaban kasa da uwa jam'iyya ta yi.

Sauran mambobin da za su iya bore nan ba da jimawa ba a kan kwamitin ayyuka na kasa na APC karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu su ne wadanda suka gudanar da aikin tantancewa da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar da ya kawo ‘yan takara a zaben 2023.

Baya ga rashin biyansu alawus-alawus, an tattaro cewa mambobin sun kosa da matakin da NWC ta yanke na rage alawus-alawus din da ba a biya ba da 40% cikin dari.

Daga bakin wani mamban da bai samu an mayar masa da kudinsa ba

Kara karanta wannan

‘Yan Takara Sun Dauko ta da zafi, Sun yi wa Atiku Abubakar alkawarin Kuri’u Miliyan 20

Wani mamban da ya janye daga takarar mataimakin shugaban APC kasa, wanda kuma aka dama dashi wajen gudanar da zaben fidda gwani a yankin Arewa maso Yamma, ya koka matuka kan wannan lamari.

Ya ce:

"Lokacin da shugaban kasa ya ba da umarnin a ranar 23 ga Maris, mutum zai yi tunanin aikin farko na wadanda suka ci gajiyar yarjejeniyar shi ne dawo da kudaden mu na takara nan take, bayan ya nemi mu rubuta bayanan bankin mu don dawo da kudaden.
“Jam’iyyar tana da kudi. Kwamitin rikon kwarya da Gwamna Buni ya jagoranta ya bar kudi, NWC ma ta samu makudan kudade, wanda ya kai biliyoyin Naira. Wane uzuri ne NWC za ta bayar na wannan jinkiri? Tun da tuni kwamitin (NWC) ya biya su alawus-alawus din.
“Da dai-dai mun nemi a mayar mana da kudadenmu, kuma mun aike da takarda kai tsaye ga kwamitin 'yan takara a taron gangamin na kasa amma duk shuru babu wani motsi.

Kara karanta wannan

Rikici: Kiristocin APC a Arewa sun ta da hankali, dole a kwace tikitin Shettima a ba su

Hakazalika, ya koka ga yadda jam'iyyar ta yi amfani da kudadensu wajen gudanar da ayyukan da ke gabanta amma ta gaza waigowa gare su domin cika alkawarin Buhari.

Ya kara da cewa:

"Don kara gishiri a raunin da muke dashi, mun kuma samu labarin cewa alawus din da ba a biyan bama an rage shi da 40% cikin dari."

Mataimakin Shugaban APC na Kasa (Arewa maso Yamma) Salihu Lukman ya yi nadamar jinkirin da aka samu, amma ya ce ana duba lamarin nan ba da jimawa za a warware.

Babu Ma’aikacin da Ke Bin Gwamnatin Yobe Bashin Ko Anini, Inji Gwamna Buni

A wani labarin, Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a ranar Juma’a ya ce gwamnatinsa na kokari wajen biyan albashin ma’aikata duk da karancin kudi da jihar ke da shi, Guardian ta ruwaito.

Buni, a wata sanarwa da babban daraktan yada labaran sa, Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu, ya ce wani bincike da wata kafar fasaha ta BudgIT ta gudanar ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC ta sanar da ranar da za ta fara gangamin yakin neman zaben Tinubu

A cewar gwamna Buni: "Rahoton binciken wanda ya tsaya a Yuli 2022, ya nuna jihar Yobe a matsayin daya daga cikin jihohin da ma'aikatan gwamnati ba sa bi bashin albashi."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.