Tsohon Shugaban PDP ya Nunawa Atiku Abin da Zai Hana Sa Kai Labari a Zaben 2023

Tsohon Shugaban PDP ya Nunawa Atiku Abin da Zai Hana Sa Kai Labari a Zaben 2023

  • Zaben zama sabon shugaban Najeriya yana karasowa, har yanzu akwai kura a jam’iyyar PDP
  • Bode George yace ya zama dole Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike su ajiye sabaninsu
  • Jagoran na PDP ya nunawa 'Dan takaran Shugaban kasar cewa yana bukatar kuri’un ‘Yan Kudu

Lagos - Bode George wanda ya taba rike kujerar mataimakin shugaban PDP na kasa a Najeriya, ya gargadi Atiku Abubakar game da takararsa a 2023.

Da aka yi hira da shi a This Day, Cif Bode George ya shaida cewa ba za ta yiwu Atiku Abubakar ya karbi mulki ba tare da kuri’un kudancin Najeriya ba.

‘Dan siyasar ya yi kira ga ‘dan takaran shugaban kasar na PDP da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas su maida wukar fadansu, su sasanta tun wuri.

A cewar tsohon Gwamnan, abin da suke so shi ne Atiku Abubakar ya tafi da kowa a zaben 2023. George yana cikin masu bakar adawa ga Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

An Gano Wanda ya yi Karambani, Ya kai Atiku da Tambuwal Kotu da Sunan Wike

Maganar Bode George

“Abin da kurum muke nema shi ne a rika damawa da mu. Dole mu shiga harkar zabe da kula da jagorancin jam’iyya.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Babu wanda zai iya lashe zabe ba tare da kuri’u masu tsoka daga yankin Arewaci ko Kudancin Najeriya ba.”
Bode George
Bode George da Atiku Abubakar Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

“Shin da gaske mu na so mu sake komawa fadar Aso Villa a 2023? Idan mu na son komawa Villa, mu na bukatar kuri’un Kudu.”

- Bode George

Babu magudi a zaben 2023

Dattijon yace kuri’un talakawa za su yi tasiri a zabe mai zuwa, don haka ya yi kira ga dukkanin 'ya 'yan jam’iyyar PDP su hada kan su domin yin nasara.

Kamar yadda Legit.ng ta kawo rahoto a ranar Litinin, Cif George yana ganin yadda hukumar INEC ta shigo da fasahar zamani, ta gyara a dokar zabe.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Rubutawa INEC Takarda, Ta Bukaci a Cafke ‘Dan Takaran APC a Katsina

“Abin ya kara bayyana yanzu da aka zamanantar da dokar zabe. An shigo da sabuwar fasaha. An jarraba sabuwar doka a zabuka uku da aka yi.
Kuma wannan ya karfafa gwiwar masu kananan shekaru da su shiryawa zabe mai zuwa.”

- Bode George

Za ayi sulhu a PDP

Rahoto yace jagororin PDP sun kafa kwamitin mutane 14 da za su sasanta rigimar da ta addabi Jam’iyyar tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike.

Ana sa ran wannan kwamiti zai duba silar rikicin, ya kuma ba Atiku shawarar hanyar da za a bi wajen samun mafita kafin lokacin takarar badi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng