NNPP Ta Rubutawa INEC Takarda, Ta Bukaci a Cafke ‘Dan Takaran APC a Katsina

NNPP Ta Rubutawa INEC Takarda, Ta Bukaci a Cafke ‘Dan Takaran APC a Katsina

  • Shugaban Jam’iyyar NNPP a Katsina yana so a kama ‘Dan takaran APC, Umar Dikko Radda
  • Hon. Sani Liti yace Dr. Umar Dikko Radda ya saba dokar zabe domin ya fara kamfe tun yanzu
  • Jam’iyyar ta na so Hukumar INEC ta hukunta ‘Dan takaran domin ya sabawa dokar Najeriya

Katsina - Jam’iyyar NNPP ta reshen jihar Katsina ta yi kira ga hukumar INEC na kasa da ta cafke ‘dan takaran APC na Gwamna, Dr. Dikko Umar Radda.

A ranar Juma’a, 12 ga watan Agusta 2022, This Day ta rahoto NNPP ta na cewa akwai bukatar hukunta Dr. Dikko Umar Radda saboda saba dokar zabe.

Shugaban NNPP na reshen jihar, Hon. Sani Liti yake cewa ‘dan takaran ya soma kamfe a kananan hukumomin Baure, Zango da Sandamu tun yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike ya Kai Atiku da Tambuwal Kotu, yace Shi ne Asalin ‘Dan takaran PDP

NNPP tace a ka’ida bai kamata ‘yan takara su fara yakin neman zaben 2023 a wannan lokaci ba.

An rahoto Sani Liti yana cewa Dr. Radda da magoya bayansa na jam’iyyar APC sun sabawa sashe na 28 (1) na dokar zabe da suka fara yakin neman zabe.

“Mun rubuto maku domin sanar da ku sabawa sashen dokar zabe da aka yi, mu na rokon a hukunta wadanda suka sabawa doka.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr. Dikko Radda
‘Dan Takaran APC a Katsina, Dr. Dikko Radda Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter
“Mu na so Mai girma Kwamishina ya tuna da abin da doka ta fada game da lokacin soma kamfe da Rose Oriaran-Anthony ta sa hannu.”

- Hon. Sani Liti

Korafin yace sai zuwa karshen Satumba zuwa farkon Oktoba za a fara kamfe, amma APC ta na kamfe a wasu garuruwa, don haka tace a cafke ‘dan takaran.

Amma shugaban yada labarai na kwamitin neman zaben APC, Ahmed Abdulkadir, ya musanya zargin, ya maida martani cewa ba su fara yawon kamfe ba.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Shiga Kamfe, APC ta Canza Tikitin ‘Yan takarar Gwamnan jihar Katsina

A wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis, Abdulkadir ya bayyana cewa Radda bai jahilci dokar zabe ba, don haka ba za zai taba sabawa dokar Najeriya ba.

“Dr. Dikko Radda bai fara yakin neman zama Gwamna ba. Abin da muka yi taro ne da shugabannin jam’iyya, iyakar ta kenan.”

- Hon. Sani Liti

Dr. Dikko Radda ya dauko Jobe

A makon nan ne aka samu labari cewa ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a APC, ya canza sunan wanda zai zama abokin takararsa a zabe mai zuwa.

Dr. Dikko Umar Radda ya dauko Hon. Faruq Lawal Jobe ya zama ‘dan takarar mataimakin Gwamna, sai aka cire sunan Alhaji Yusuf Aliyu Musawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel