Gwamna Lalong: Ina Alfahari da Jagorantar Tafiyar Tinubu da Shettima Duk da Ni Kiristan Katolika Ne

Gwamna Lalong: Ina Alfahari da Jagorantar Tafiyar Tinubu da Shettima Duk da Ni Kiristan Katolika Ne

  • Gwamnan jihar Filato ya bayyana kwarin gwiwarsa na ci gaba da tallata dan takarar shugaban kasa na APC
  • Kiristocin Najeriya sun nuna damuwa game da zabo Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Bola Tinubu
  • Jam'iyyar APC ta sanar da ranar da za a fara gangamin tallata Tinubu da Shettima gabanin zaben 2023

Jihar Filato - Gwamna Simon Lalong na jihar Filato a ranar Laraba ya soki Kiristocin da ke adawa da amincewarsa ta zama babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na APC.

Lalong ya bayyana cewa a matsayinsa na kiristan Katolika da ya samu lambar yabo ta Paparoma, shi Paparoman bai ce masa abin da ya yi ba daidai bane.

Bayan fitowar Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya zabi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa, rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Terhemen Anongo: Dalibin da Ya Bar Karatun Likitanci a Aji 5, Ya kare a Turin Baro

Paparoma bai hana ni tallata Tinubu da Shettima ba, inji Lalong
Gwamna Lalong: Ina Alfahari da Jagorantar Tafiyar Tinubu da Shettima Duk da Ni Kiristan Katolika Ne | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wannan zabi dai ya haifar da cece-kuce, musamman a tsakanin mabiya addinin Kirista da suka hada da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) wadanda tun daga lokacin suka ki amincewa da tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa ya kare dalilinsa na zabar Shettima a matsayin mataimaki, masu suka sun jajirce wajen la'akari da akida da addinan 'yan Najeriya.

Sai dai, gwamna Lalong ya goyi bayan ra'ayin tikitin Musulmi da Musulmi bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake Abuja.

Ni babban jigo ne a addinin kirista, inji Lalong

A cikin tambayoyin da amsa, Lalong ya ce a matsayinsa na wanda ya lashe kyautar Knight na Saint Gregory, ya kasance mai kishin Katolika duk da sabon matsayin da ya karba na tallata tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Gwamna Lalong ya ci gaba da cewa yana matukar mutunta addininsa a matsayinsa na Kirista, inda ya yi nuni da cewa an zabe shi gwamna ne na dukkan addinai; Musulmi da Kirista, Daily Trust ta naqalto.

Gwamnan na Filato ya ce saboda haka bai da tabbacin daga ina masu ikirarin kiristoci ne kuma suke adawa da nadin nasa.

Ya tunatar da su cewa a lokacin da ya koma Jos bayan an nada shi a matsayin DG na kungiyar tallata Tinubu, kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar ta yi masa maraba.

APC Za Ta Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Ranar 28 Ga Satumba

A wani labarin, bayan wasu sauye sauyen tsare-tsare, jam’iyyar APC ta bayyana shirin fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Satumba.

A yau ne aka shirya gudanar da taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na APC karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, domin yanke shawara kan ranar da kuma shirya taron kwamitin zartarwa (NEC) na jam’iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa A Rikicin PDP, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Cimma Wata Matsaya Ɗaya

Bincike ya nuna cewa a taron karshe da NEC ta APC ta gudanar a watan Afrilu, ta mika ragamar mulki ga kwamitin ta na NWC na tsawon kwanaki 90, Tribune Online ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel