Terhemen Anongo: Dalibin da Ya Bar Karatun Likitanci a Aji 5, Ya kare a Turin Baro

Terhemen Anongo: Dalibin da Ya Bar Karatun Likitanci a Aji 5, Ya kare a Turin Baro

  • Terhemen Anongo matashi ne mai shekaru 43 wanda ya bar makarantar karatun likitanci yayin da yake aji biyar, yana shakar kamshin kammalawa
  • Ya sanar da cewa, mahaifinsa ne ya tirsasa shi karantar likitancin amma shi Injiniyanci yaso karanta, lamarin da ya haifar masa da ciwon damuwa
  • Terhemen ya so komawa makaranta bayan wani lokaci, sai dai bai samu dama ba, shiyasa ya runguma sana'ar turin baro a Gboko dake jihar Benuwe

Terhemen Anongo dalibi ne mai hazaka da ke son darasin Physics da Lissafi. Ya kammala makarantar sakandare da sakamako mai matukar kyau. Yana fatan zama Injiniyan man fetur a baya.

Sai dai, mahaifinsa Anongo malamin lissafi ne kuma yana shiryawa 'dan shi wani abu daban. Yana son ya karanci likitanci kuma ya zama cikakken likita.

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 5 da za su taimakawa Peter Obi a kan Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Terhemen Anongo
Terhemen Anongo: Dalibin da Ya Bar Karatun Likitanci a Aji 5, Ya kare a Turin Baro. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Tushen mummunan labarin Terhemen

A 1996, lokacin da Terhemen ya shiga jami'ar Ibadan domin karantar likitanci, Anongo ya fara tsammanin burinsa na ganin hazikin dansa a matsayin likita zai tabbata, zai zama daya daga cikin likitoci masu nasara a kasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abun takaici, kaddarar da rayuwar Terhemen ke kunshe da ita shine ya zama mai turin baro a garin Gboko na jihar Benuwe.

A tattaunawa da The Punch da Terhemen yayi, wanda yanzu shekarunsa 43, ya bayyana yadda komai ya rikice masa. Ya shiga jami'ar a zangon karatu na 1996/97. Tsakanin 1996 zuwa 1999, komai ya tafi daidai. A shekarar 2000, ya tafi asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan, UCH kasancewarsa a aji 5.

Tsananin damuwa

A lokacin da ya kusa cika burin mahaifinsa, Terhemen ya gaza da damuwa kuma baya kaunar karatun likitanci da yake yi. Ya yi abinda ba a taba tsammani ba, ya bar makaranta.

Kara karanta wannan

Mafi tsufa a raye: An gano wani tsoho dan Najeriya mai shekaru 126 a raye kuma da karfinsa

"Duk da a wani lokacin na yi kokarin komawa, amma hukumomi sun hana ni," ya sanar da Punch.

Ciwon damuwa tana taba kwakwalwa

Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya, WHO ta bayyana, ciwon damuwa yana farawa ne da takaici, takura, tsoro da mutane ke fuskanta lokaci bayan lokaci a rayuwarsu.

Mene ne ya kawowa Terhemen ciwon damuwa?

Terhemen ya bayyana cewa, bai taba son karantar likitanci ba. Ya kammala sakandare da sakamako mai kyau da kuma kauna ta musamman a Physics da lissafi. Ya so karantar injiniyanci. Sai dai mahaifinsa ya ki barinsa inda yace wasu malaman Indiya sun sanar masa cewa karatu mai kyau shine likitanci.

A kalamansa: "Amma lokacin da na shiga makaranta, na gane cewa hadda ne likitanci, haddace kalaman da baka san tarihinsu ba. Hakan yasa raina ya fita daga karantun duk da har na kai ga zuwa asibitin koyarwa."

Terhemen ya alakanta damuwarsa da rashin jin dadin zamansa a jami'ar Ibadan.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

"Yanayin jami'ar da tsarinta, jama'ar basu da sabo, duk da ita ce makarantar koyon likitanci mafi inganci," yace.

Dalibin likitancin da ya koma turin baro

Bayan kokarinsa na komawa makaranta duk ya gagara, Terhemen yanzu yana rayuwa a Gboko jihar Benuwe, inda yake samun na abinci da sana'ar turin baro.

"Ka yi tunani, dalibin likitanci wanda da yanzu ya kammala karatu amma yake wannan aikin. Sa'o'i na duk sun zama kwararru amma ni ina turin baro. Ka gwada irin damuwar da mutumin zai shiga," ya koka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel