2023: Fasto A Najeriya Ya Tsige Danuwansa Daga Mukaminsa A Coci Saboda Goyon Bayan 'Dan Takarar Shugaba Kasa'

2023: Fasto A Najeriya Ya Tsige Danuwansa Daga Mukaminsa A Coci Saboda Goyon Bayan 'Dan Takarar Shugaba Kasa'

  • Fasto Chris Oyakhilome ya dakatar da dan uwansa daga mukaminsa a matsayin shugaban sashin kirkire-kire na Loveworld Next
  • Faston ya kuma dakatar da dukkan danginsa daga rike mukamai a cocin nasa
  • Ya kuma umurci a tura dan uwansa nasa zuwa ya tafi hutun 'sauya tunani' saboda alaka da wasu yan siyasa gabanin babban zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Opebi - Wanda ya kafa cocin Christ Embassy Ministry, Fasto Chris Oyakhilome ya dakatar da dan uwansa, Daysman Oyakhilome Woghiren, daga mukaminsa a matsayin shugaban Loveworld Next da Loveworld Innovation.

Fasto Chris Oyakhilome.
2023: Babban Fasto A Najeriya Ya Dakatar Da Danuwansa Daka Mukaminsa A Coci Saboda Goyon Bayan Dan Siyasa. Hoto: Photo credit: Love World Media.
Asali: Instagram

Ana zargin dakatarwar ba za ta rasa nasaba ba da alaka da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jirgin Sojojin NAF Ya Halaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, Oyakhilome ya ce:

"An cire wannan mutumin, Oyakhilome Woghiren daga mukaminsa na shugaban Loveworld Next da Loveworld Innovation an kuma dakatar da shi daga dukkan ayyukansa na ofis saboda halayya marasa kyau.
"Zan saka shi a shirin sauya tunani daga yanzu ba tare da bata lokaci ba."

An ga wasu takardu da ke nuna hoton Tinubu da Woghiren da wasu jami'an APC a wani yanayi da ya yi kama da yana goyon bayansu.

Oyakhilome, dan shekara 58, galibi ba a san shi da shiga harkar siyasa ba ko yin tsokaci kan siyasar Najeriya.

2023: Kungiyar Kirista Ta Watsa Wa CAN Kasa A Ido, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi

A wani rahotonn, wata kungiya, mai suna 'Christ Shiloh Ambassadors of Nigeria', ta ce ba laifi bane domin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya zabi musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas, ya zabi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar sa. Sassa da dama na kasar sun nuna rashin jin dadin su game da zabin.

A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Pastor Ade Odudola da sakataren ta, Pasto Felix Rawa, suka fitar bayan babban taron su da suka raba wa manema labarai, kungiyar ta ce ba addinin bane ya kamata ya zama abin duba wa wurin zaben shugabanni a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164