Ana zargin ‘Dan Takaran Shugaban kasa da Shiga ‘kungiyar asiri’, Ya Kare Kan Shi

Ana zargin ‘Dan Takaran Shugaban kasa da Shiga ‘kungiyar asiri’, Ya Kare Kan Shi

  • Ana zargin ‘dan takaran LP, Peter Obi yana da alaka da kungiyar Pyrates Confraternity
  • Hadiminsa, Valentine Obienyem ya karyata wannan zargi, yace Obi bai da wani hadi da tafiyar
  • Valentine Obienyem ya kawo karshen jifan Obi da Namadi Sambo da aka yi da wannan zargin

Lagos - Valentine Obienyem wanda yake magana da yawun Peter Obi, yace ‘dan takarar shugaban kasar bai da alaka da tafiyar Pyrates Confraternity.

Valentine Obienyem ya aikawa The Cable sako ta waya bayan an bukaci jin ta bakinsa game da dangantakar Peter Obi da wannan kungiya a Najeriya.

Wani mutumi mai suna Fejiro Oliver a shafin Facebook, ya yi ikirarin cewa Peter Obi yana cikin ‘yan wannan kungiya ta su watau Pyrates Confraternity.

Shi dai Oliver yace suna tare da Obi a wannan tafiya, ya kuma ce ‘dan siyasar ya tabbatar ya kurbi ruwan kungiyar a lokacin da yake mulki a Anambra.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Daga baya Mista Fejiro Oliver ya goge maganar a Facebook, amma ya jawo alamar tambaya a kan Obi wanda yake neman zama shugaban Najeriya a LP.

Rahoton da jaridar ta fitar a yammacin Litinin ya nuna Hadimin ‘dan takaran yace sam Obi bai da wata alaka da kungiyar nan kamar yadda ake rayawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi
Peter Obi da wasu masoyansa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Namadi Sambo yana tare da su?

A wannan bidiyo da ya rika yawo a Facebook, an jefi Namadi Sambo da zargin shi ma yana cikin manyan ‘ya ‘yan wannan kungiya da ta fi karfi ne a Kudu.

Namadi Sambo ya rike kujerar mataimakin shugaban kasar nan tsakanin 2010 da 2015. Har zuwa yanzu tsohon gwamnan bai yi magana kan batun ba.

Ina aka samo Pyrates Confraternity?

Shekaru kusan 70 da suka shude aka kafa kungiyar National Association of Seadogs (NAS) wanda aka fi sani da Pyrates Confraternity a kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Sanata da Gwamnan APC Ya Shiga Uku, An Rufe Shi a Gidan Yari

Wole Soyinka, Ralph Opara, Pius Oleghe, Ikpehare Aig-Imoukhuede, Nathaniel Oyelola, Olumuyiwa Awe da Sylvanus U. Egbuche suka kafa ta a 1952.

A lokacin an fito da kungiyar ne domin magance matsalolin da suka addabi mutanen Najeriya.

Yanzu wasu suna zargin NAS ta zama tamkar kungiyar 'yan asiri. Amma a wata shari'a da aka yi a Ribas, Alkali ya nesanta kungiyar da zama ta asiri.

PDP zuwa LP

Kuna sane cewa yanzu Peter Obi da Atiku Abubakar duk kowa ya kama hanyar gabansa, daya zai yi takara a PDP, dayan zai jarraba sa’a a LP a 2023.

An ji labari cewa da Peter Obi ya tashi shiga Jam’iyyar LP, ko Atiku Abubakar wanda ya fara dauko shi a zaben 2019 bai san yana shirin sauya-sheka ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng