Tsohon Gwamnan APC Ya Fasa-kwai, Yace da Magudi Jam’iyyarsa ta ci Zabe a 2019

Tsohon Gwamnan APC Ya Fasa-kwai, Yace da Magudi Jam’iyyarsa ta ci Zabe a 2019

  • Ibikunle Amosun ya shaidawa Duniya cewa murdiya aka yi domin APC ta cigaba da mulki a Ogun
  • Tsohon Gwamnan yace ‘Dan takaran APM ya lashe zaben jihar Ogun, amma ‘Yan APC suka murde
  • Sanata Amosun ya nuna har gobe bai tare da Gwamna Dapo Abiodun, yace dole ayi waje da shi a 2023

Ogun - Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yace Gwamna mai-ci, Dapo Abiodun ya lashe zabe a 2019 ne ta hanyar magudi da murdiya.

Punch ta ce Sanata Ibikunle Amosun ya bayyana wannan ne a lokacin da aka ba shi lambar yabo a wajen taron da kungiyar Abeokuta Club ta shirya.

A ranar Juma’a, 5 ga watan Agusta 2022, Abeokuta Club tayi bikin cika shekara 50 da kafuwa.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Basarake Ya Zage Yana Yi wa Bola Tinubu da Gwamnan APC Kamfe

Ibikunle Amosun ya yi wa APC zagon-kasa a zaben gwamnan jihar Ogun a 2019, ya marawa Adekunle Akinlade baya wanda ya yi takara a inuwar APM.

APC ta murde kuri'u 19, 000

Adekunle Akinlade ya sha kasa ne a hannun Abiodun da tazarar kuri’un da ba su kai 20, 000 ba. Tsohon gwamnan yake cewa da magudi aka lashe zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar APC da Abiodun sun samu kuri’a 241,670 yayin da ‘dan takarar jam’iyyar hamayyar, Akinlade ya tashi da kuri’a 222,153 a zaben da ya wuce.

A cewar Amosun wanda Sanata ne yanzu haka, an yi magudin ne domin ganin jam’iyyar APC ta cigaba da mulki a Ogun daga 2019 zuwa Mayun 2023.

“A zaben da ya wuce, na godewa Allah, Cif Osoba yana nan, na fada cewa mun ci zabenmu da kyau. Sai suka yi magudi, suka tashi da kuri’u 19, 000.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Wasunsu sun zo sun bani hakuri. Ba zan ambaci sunan kowa ba. Mun yi nasara a zaben nan. Amma na hakura.”
“Mun yi aikinmu. Za mu cigaba da yin abin da za muyi. Ubangiji zai kasance tare da mu. Na yafe, amma ban tare da Abiodun."

- Ibikunle Amosun

Sai an sauke Abiodun a 2023

Duk da abin da ya faru a zaben magajinsa, Amosun yace ya hakura domin wadanda suka yi wannan danyen aiki na tafka magudi, sun nemi ya yafe masu.

Sanatan yace ya yi afuwa, amma hakan ba zai hana shi yi wa Gwamnan adawa ba.

Daily Trust ta rahoto tsohon ‘dan takaran shugaban kasan yana cewa bai goyon bayan gwamnatin Abiodun, kuma dole su yake ta a zabe mai zuwa da za ayi a 2023.

Tsige shugaban kasa

Dazu rahoto ya zo maku cewa wasu daga cikin wadanda suka fi kowa kaunar Muhammadu Buhari a baya, sun fito suna kira ga Majalisa ta tunbuke shi

Kara karanta wannan

Ana Zargin Shugaban Jam’iyya Ya Dauki Mataki ba da Sanin Sauran Shugabannin APC ba

Wani malamin jami’a a Katsina yake cewa sun gwammace su zauna ƙarƙashin mulkin Fasto mai tausayi da jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel