2023: Tinubu Ya Nada El-Rufai Da Oshiomhole Manyan Mukamai A Kungiyar Kamfen Dinsa
- Gabanin babban zaben shugaban kasa na 2023, dan takarar shugaban kasa na APC yana cigaba da shirin kamfen dinsa
- Tinubu da tawagarsa a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli sun sanar da karin wasu mutane a tawagar
- An nada Adams Oshiomhole da Mallam Nasir El-Rufai matsayin Ciyaman da Direkta-Janar na kamfen din Tinubu
An zabi Mallam Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna da Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Jihar Edo domin jagorantar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.
An nada Oshiomhole a matsayin ciyaman na kungiyar kamfen din Tinubu, yayin da Nasir El-Rufai aka na shi direkta janar na kungiyar yakin neman zaben.
Shafin kungiyar kafar watsa labarai masu goyon bayan Tinubu, TMS, ce ta sanar da nadin a shafinta na Twitter @TinubuMediaS kamar yadda Legit Hausa ta gani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana daukan Oshiomhole da Tinubu a matsayin wadanda ke cikin mutanen da aka kafa jam'iyyar APC tare da su a 2014.
Tun bayan kafa jam'iyyar, mutanen biyu sun rike mukamai daban-daban inda Oshiomhole ya rike mukamin shugaban jam'iyyar na kasa bayan yin gwamna a Edo.
Shi kuma El-Rufai shine gwamna mai ci yanzu a Jihar Kaduna kuma ya taka muhimmiyar rawa wurin nasarar Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki.
2023: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Kan 'Fastocin Bogi'
A wani rahoton, Jam'iyyar PDP ta bukaci dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, nan take ya janye takararsa saboda ikirarin cewa ya dako hayar 'Bishop Bishop' na bogi su hallarci kaddamar da mataimakinsa, Kashim Shettima, rahoton Daily Trust.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma'a, sakataren watsa labaran jam'iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce Tinubu da APC sun aikata babban laifi kuma tare da yaudara, ya kara da cewa ba su cancanta shiga zaben ba.
Asali: Legit.ng