Na dawo daga rakiyarka: Sanatan arewa ya janye daga tawagar kamfen din Tinubu saboda tikitin Musulmi da Musumi
- Sanata Ishaku Abbo ya dawo daga rakiyar Asiwaju Bola Tinubu kan daukar Musulmi dan uwansa, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa
- Abbo ya ce ya yi murabus daga kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC)
- Sanatan ya ce kungiyarsa ta yanke cewa kada Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin mataimakinsa amma sai ya yi watsi da batun
Abuja - Sanata mai wakiltan yankin Adamawa ta arewa, Ishaku Abbo, ya yi murabus daga kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Abbo ya bayyana daukar tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima wanda ya kasance Musulmi da Tinubu ya yi don ya zama abokin takararsa a matsayin rashin tunani tsantsa.
Sanatan ya bayyana matsayinsa kan abokin takarar Tinubu ga manema labarai a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, a Abuja, jaridar Punch ta rahoto.
Tinubu bai yi koyi da Shugaba Buhari ba
Ya kuma kara da cewar ya gana da wata kungiyar goyon bayansa a Abuja a kokarin nemawa Tinubu abokin takara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kungiyar ta yanke cewa bai kamata Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin abokin takararsa ba a zaben shugaban kasa na 2023.
Sanatan ya ce Tinubu ya ki yin koyi da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya dauki kirista a matsayin abokin takararsa a 2015.
Pulse ta nakalto Abbo yana cewa:
“Ga Tinubu da aka baiwa tikiti a yanzu sannan ya juya ya yi abun da ya kasa cimma a 2015 duk da adawa daga yan Katolika da sauran shugabannin kirista rashin tunani ne tsantsa.
“Buhari ya yi yakin basasa kuma ya fahimci illar kasa da ta rabu. Lokacin da Tinubu ya so zama mataimakin shugaban kasa a 2015, Buhari ya ce a’a saboda ya fahimci muhimmancin hadin kai.
“Mun zauna a Abuja sannan muka shirya dabaru muka kuma yanke cewa kada ya dauki Musulmi a matsayin abokin takara. Shi (Tinubu) ya yi watsi da rahoton.
“Zuciyata ba za ta barni na yiwa Tinubu kamfen ba. Ni dan kungiyar CAN ne; ba zan iya watsi da CAN ba. Ina nan a APC. Amma ba zan wofantar da kasata bisa la’akari da siyasa ba."
Ba zan yarda da tikitin Kirista da Kirista ba – Sanata Abbo
Sanata Abbo ya kuma bayyana cewa kamar yadda yake adawa da tikitin Musulmi da Musulmi, ba zai yarda da tikitin Kirista da Kirista ba saboda hakan ba zai yiwa Musulmai dadi ba suma.
“Ba za mu iya yi wa irin wannan mutumin aiki ba. Zan yi adawa da tikitin Kirista da Kirista saboda ina sha'awar zaman lafiyar kasar. Tikitin Kirista da Kirista zai zama abin damuwa ga Musulman kasar nan.
“Kasar ta rabu sosai a tsakanin Musulmi da Kirista. Don haka duk gwamnatin da ta kasance Musulmi da Musulmi, za ta zama ba bisa ka’ida ba, kuma ba za ta taba samun girmamawar Kirista ba.”
Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima
A gefe guda, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Borno, Bishop Mohammed Naga, ya yaba da zabar tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima da aka yi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya sanar da Shettima a matsayin abokin takararsa a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, duk da adawa da aka dunga nunawa kan tikitin Musulmi da Musulmi.
Asali: Legit.ng