2023: PDP ta yi dabara, ta zabo wanda zai kawo karshen APC a Gombe, inji tsagin dan takara

2023: PDP ta yi dabara, ta zabo wanda zai kawo karshen APC a Gombe, inji tsagin dan takara

  • Yayin da zabe ke karatowa, jam'iyyar PDP ta sha yabo bisa zabo dan takarar da zai gwabza a zaben gwamnan Gombe
  • Hakazalika, tsagin dan takarar ya kuma bayyana irin abubuwan da zai sa a gaba matukar ya samu damar mulkar jihar a 2023
  • A bangare guda, tsagin ya yi kira ga jama'ar jihar da su nemo katin zabe domin lallasa jam'iyyar APC

Jihar Gombe - Jam’iyyar PDP a Gombe ta sha yabo kan zaben tsohon Manajan Darakta kuma Shugaban Bankin Sun Trust, Jibrin Muhammad Barde, a matsayin dan takarar Gwamna a 2023.

Wata sanarwa da ofishin yada labaransa ta fitar a ranar Alhamis ta ce Barde a matsayinsa na mutum mai ilimin kudi zai gudanar da gwamnati mai cike da tsarin kasafin kudi tare da ba da fifiko kan tsare-tsaren mutane idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki

Dan takarar gwamna ya yaba yadda PDP ta bashi dama
2023: PDP ta yi dabara, ta zabo wanda zai kawo karshen APC a Gombe, inji tsagin dan takara | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust ya kuma ce, sanarwar ta ce makomar jihar da zaman lafiyar al’ummarta su zai sa a gaba ba wai cika aljifan wasu ‘yan tsiraru tare da kashe miliyoyin mutanen Gombe.

Sanarwar ta kara da cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Abu ne mai sauki a gare mu mu tallata takararsa saboda irin abubuwan da yake da su da kuma tausaya wa jama’a.
"Ga wani mutum wanda a tsawon shekarun da suka wuce ya tallafawa maza da mata, yara da manya ta fuskoki daban-daban.
“Muna kira ga daukacin mutanen mu da su fito kwan su da kwarkwata domin yin rijistar katin zabe tare da karbarsa domin su samu damar yin amfani da karfin ikonsu wajen aika gwamnatin APC waje ta girbi abinda da ta shuka.”

2023: 'Yan Najeriya sun kagu a fatattaki APC a kasa, inji dan takarar NNPP Kwankwaso

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ban dauki Sanata Datti a matayin abokin takarata ba, in ji Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Alhaji Rabi’u Kwankwaso, ya ce daga dukkan alamu ‘yan Najeriya sun gaji da jam’iyyar APC mai mulki, kuma suna da burin ganin karshen gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwankwaso ya yabawa dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa a jihar Gombe da yammacin ranar Asabar, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama da ke nuna cewa jama’a a shirye suke don samun damar kawar da gwamnatin APC a zaben 2023, inji Arise Tv.

Kwankwaso, wanda ya je Gombe domin kaddamar da ofishin jam’iyyar, ya ce dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa daga filin jirgin sama zuwa cikin garin, sun zaburar da shi cewa jihar Gombe ta shiga sahun su Kano wajen jihohin Kwankwasiyya.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a otal din Gombe na kasa da kasa, jim kadan bayan kaddamar da ofishin, Kwankwaso ya ce akwai manyan alamu na kyakkyawar makoma ga jam’iyyar da ba ta kai watanni hudu ba da yin kaurin suna.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

A wani labarin, a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu 2022, tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya samu nasara a zaben tsaida gwani.

Daily Trust ta ce Ibrahim Hassan Dankwambo shi ne wanda jam’iyyar PDP ta ba takarar Sanata na yankin Arewacin jihar Gombe a zabe mai zuwa.

Tsohon gwamnan ya yi galaba ne a kan Sanata Usman Bayero Nafada da Abdulkadir Hamma Saleh, wanda suka hakura, suka janye masa takarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.