Babbar magana: Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki

Babbar magana: Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki

  • 'Yan bindiga sun hallaka wani jami'in tsaro da ke tare da dan takarar mataimakin gwamna a jihar Ribas
  • An farmaki dan takarar mataimakin gwamnan ne yayin da ya fito daga wani taro, kamar yadda rahoto ya kawo
  • Rundunar 'yan sanda sun tabbatar da farmakin, sun kuma bayyanamatakin da ake dauka a yanzu

Jihar Ribas - Dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ribas, Dokta Innocent Barikor, ya tsallake rijiya da baya a wani harin da aka kai masa a Fatakwal, babban birnin jihar.

Sai dai an tattaro cewa, ‘yan bindigar sun kashe ‘yan sandan da ke bayansa nan take, inji rahoton The Nation.

Yadda dan takarar mataimakin gwamna ya tsallake rijiya da baya
Babbar magana: Dan takarar tataimakin gwamna ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An ce Barikor ya bar ofishinsa da ke GRA ne a daren ranar Talata domin wani taro a wani wuri da ba a bayyana ba ba tare da sanin cewa wasu ‘yan bindiga na jiransa a waje ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Dukkan kasurguman 'yan Boko Haram da ke daure a Kuje sun tsere, inji minista

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce da ganin Barikor ‘yan bindigar suka bude wa tawagarsa wuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar majiyar:

“Barikor ya tserewa mashekan amma jami’in dan sandansa bai yi sa’a ba saboda harsashin da suka harba ya kashe shi nan take.”

Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Darlington Nwauju, ya tabbatar da faruwar harin.

Nwauju ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin inda ya nemi babban sufeton ‘yan sanda da ya binciki lamarin.

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO), DSCP Grace Iringe-Koko, ta ce bata san batun da shiryayyen kisan ba, rahoton Punch.

Ta ce:

“Ba shiryayyen kisa ba ne. An dai kashe sanda. Ina tsammanin shi ne abin ya faru saboda sun gan shi da bindiga. Babu wani abu da ya faru da dan takarar. Muna kan binciken lamarin kuma an kewaye wurin.”

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce Najeriya ta cikin matsanancin yanayi

An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

A wani labarin, da alamu wasu manyan fursunoni a gidan yari na Kuje da ke Abuja sun tsere a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Talata, inji rahoton The Nation.

Harin da ya dauki tsawon sa'o'i kadan, an ce jami'an soji da masu gadin gidan yarin da ke bakin aiki sun yi artabu da tsagerun.

Majiyoyi sun ce mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da abokan harkallarsa da ke wurin, mai yiwuwa sun tsere daga magarkama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel