Shugaban kasa a 2023: Ban dauki Sanata Datti a matsayin abokin takarata ba, in ji Peter Obi

Shugaban kasa a 2023: Ban dauki Sanata Datti a matsayin abokin takarata ba, in ji Peter Obi

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party ya karyata rade-radin cewa ya zabi Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakinsa
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya jadadda cewa har yanzu suna kan tattaunawa da mutane da dama kan wanda zai zama abokin takararsa
  • Sanata Baba-Ahmed ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa na PDP amma sai ya janye tun kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya karyata rahotannin cewa ya dauki Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin abokin takararsa na babban zaben 2023.

Obi ya bayyana hakan ne a yayin da ake hira da shi a Arise TV a safiyar ranar Laraba, 6 ga watan Yuli.

Peter Obi
Shugaban kasa a 2023: Ban dauki Sanata Datti a matayin abokin takarata ba, in ji Peter Obi Hoto: The Cable
Asali: UGC

Sai dai kuma, tsohon gwamnan na jihar Anambra bai ambaci sunan ainahin wanda zai zamo abokin takararsa a zaben mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce Najeriya ta cikin matsanancin yanayi

Ya dai jadadda cewa suna kan tattaunawa da mutane daban-daban saboda yana so wanda zai zama mataimakinsa ya kasance ya fi shi karancin shekaru, rahoton Nigerian Tribune.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baba-Ahmed mai shekaru 46 ya kasance dan kasuwa kuma dan siyasa wanda ya fito daga jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Daga shekarar 2003 zuwa 2007, ya rike mukamin dan majalisar wakilai. An kuma zabe shi a matsayin sanata mai wakiltan Kaduna ta arewa a watan Afrilun 2011 karkashin inuwar jam’iyyar Congress for Progressive Change.

Ya kuma kasance dan jam’iyyar Peoples Democracy Party kuma daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa har zuwa watan Mayu, inda ya janye daga tseren kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Peter Obi: A madadin kwararru, 'yan tasha ne ke tafiyar da lamurran kasar nan

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

Mun ji cewa Peter Obi, ya ce yan tasha ne ke jan ragamar harkokin Najeriya maimakon a samu kwararrun masu lasisi.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kara da cewar abubuwan farko da yan Najeriya ke dubawa a yayin zabe shine ya jefa kasar a halin da take ciki a yanzu.

Dan takarar shugaban kasar ya ja hankalin yan Najeriya da su tabbata sun zabi dan takarar da ya cancanta a 2023 domin jan ragamar al’amuran kasar, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel