Bikin sauya sheka: Dan majalisa ya fice daga APC, ya shige inuwar leman PDP
- Jam'iyyar APC ta yi zakkan dangi yayin da fitaccen mamba a majlisar dokokin jihar Oyo ya sauka sheka zuwa PDP
- Hakazalika, dan majalisar ya kuma bayyana dalilin komawarsa, kana ya ce magoya bayansa sun bi sahunsa
- A bangare guda, ya bayyana irin tagomashin da shirya wa jam'iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa a jihar da kasa baki daya
Jihar Oyo - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ogo-Oluwa/Surulere a majalisar dokokin jihar Oyo, Honarabul Simeon Oyeleke ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, inji rahoton Tribune Online.
Oyeleke, wanda aka zaba a majalisar wakilai ta yanzu a karkashin jam’iyyar APC ya bayyana matakin nasa ne a ranar Laraba 6 ga watan Yuli, 2022.
Oyeleke dai ya bayyana dalilin ficewarsa ne ga gazawar jam’iyyar APC a jihar Oyo wajen tabbatar da adalci da daidaito wajen mu’amala da 'yan jam’iyyar.
Ya ce ya koma PDP ne saboda ta nuna kwazo sosai a jihar Oyo kuma ita ce jam’iyyar da za ta iya doke APC a dukkan matakai a 2023, rahoton Ripples Nigeria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyeleke ya ce:
“Yanzu ni dan jam’iyyar PDP ne ba dan jam’iyyar APC ba. Wannan a hukumansce kenan. Dubban magoya bayana sun koma PDP tare da ni.
“A gaskiya, mun yanke shawarar ne tare da magoya bayana. Ba zan iya ci gaba da kasancewa a cikin jam'iyyar siyasar da ba ta mutunta ka'idoji da akidar dimokuradiyya ba tare da daraja sha'awar siyasa ta ba."
Dan majalisar ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da gwamna Seyi Makinde, da sauran shugabannin PDP, da ‘yan mazabarsa domin tabbatar da cewa jam'iyyar ta rike madafun iko da dama a jihar da ma kasa baki daya.
Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki
A wani labarin, dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ribas, Dokta Innocent Barikor, ya tsallake rijiya da baya a wani harin da aka kai masa a Fatakwal, babban birnin jihar.
Sai dai an tattaro cewa, ‘yan bindigar sun kashe ‘yan sandan da ke bayansa nan take, inji rahoton The Nation.
An ce Barikor ya bar ofishinsa da ke GRA ne a daren ranar Talata domin wani taro a wani wuri da ba a bayyana ba ba tare da sanin cewa wasu ‘yan bindiga na jiransa a waje ba.
Asali: Legit.ng