Shiru-shirun Wike ya birkita Atiku, kan jagororin jam’iyyar PDP ya rabu kafin a je ko ina

Shiru-shirun Wike ya birkita Atiku, kan jagororin jam’iyyar PDP ya rabu kafin a je ko ina

  • Gwamna Nyesom Wike ya koma gefe ya yi gum a PDP, ya ki fitowa ya goyi bayan Atiku Abubakar
  • Na kusa da Wike su na cewa ya zama dole ayi waje da Iyorchia Ayu daga kujerar shugaban Jam’iyya
  • Takarar Atiku Abubakar na fuskantar barazana idan bai shawo kan ‘yan bangaren Gwamnan Ribas ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa gum din da Nyesom Wike yake yi tun bayan zaben fitar da gwani, ya damalmala abubuwa a jam’iyyar PDP.

Rashin jituwar Gwamna Nyesom Wike da Atiku Abubakar ya na barka PDP a kudancin Najeriya. Bugu da kari Wike ya ki bari ya zauna da mutanen Atiku.

Manyan wadanda ke goyon bayan Gwamnan irinsu Okezie Ikpeazu, Seyi Makinde, Samuel Ortom, da Ayodele Fayose sun nuna fushinsu ga Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa daraktan fim din Izzar So, Nura Mustapha Waye rasuwa

Duk abin da ake yi, Wike ya yi tsit wanda hakan ta sa ake tunanin zai iya sauya sheka zuwa APC, LP ko NNPP, ko akalla ya ki taimakawa PDP a zaben 2023.

Kai ya rabu a PDP

Kan kusoshin PDP a kudancin Najeriya ya rabu tun da Atiku ya tsaida Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa, wasunsu su na adawa da wannan zabin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton Daily Trust ya nuna Atiku da Okowa na fuskantar barazana a jihohin irinsu Delta, Edo, Akwa Ibom, Bayelsa, Legas, Ogun, Ondo, Anambra zuwa Imo.

Amma a jihohin Ribas, Kuros Riba, Enugu, Abia, Oyo da Ekiti, ‘ya ‘yan PDP ba su gamsu da Okowa ba. Masana su na ganin hakan zai iya kawowa PDP cikas.

Atiku da Gwamna Ifeanyi Okowa
Ifeanyi Okowa tare da Atiku Abubakar Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

Sai an tunbuke Ayu

The Nation ta ce mutanen Nyesom Wike sun bukaci shugaban PDP na kasa watau Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerarsa a matsayin sharadin farko na yin sulhu.

Kara karanta wannan

Barakar PDP ta ki dinkewa, Wike ya yi watsi da wanda Atiku ya tura kasar waje ayi sulhu

Ba dole ba ne 'dan takaran da sauran 'yan PDP su yarda a sauke shugaban jam'iyyar haka kurum.

Idan abubuwa suka tafi a haka, Atiku Abubakar ba zai kai labari a a zabe mai zuwa a jihohin da suka fi ko ina yawan kuri’u a Najeriya ba; Ribas, Legas da Kano.

Bukola Saraki yana kokarin dinke barakar da ta taso, tsohon shugaban majalisar yana bi yana lallaban Wike da mutanen na sa, su marawa Atiku Abubakar baya.

Wasu tsofaffin gwamnoni da tsofaffin Ministoci da wadanda aka kafa PDP da su, duk su na goyon bayan Atiku, amma akwai bangaren da su na bayan Gwamnan ne.

Irinsu Tsohon Gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, tsohon Ministan shari’a, Mohammed Bello Adoke, ‘yan majalisu da-dama ba su tare da Atiku.

BOT ta tsoma baki

Majalisar amintattu na BOT ta dauki mataki domin sasanta rigimar da ke neman barkewa a PDP. A farkon makon nan aka tabbatar da wannan labari a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙura ba ta lafa ba, Amintaccen jigon PDP ya magantu kan ganawar Wike da Tinubu a Faransa

Shugaban BOT, Walid Jibrin ya tabbatar da cewa an kafa kwamitin da zai zauna da Nyesom Wike. 'Dan takaran PDP a 2023 ne zai jagoranci wannan kwamiti da kan shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel