Atiku Abubakar da Gwamnoni 13 za su ziyarci Wike a shirin lallashin Gwamnan kafin 2023
- Majalisar amintattu na BOT ta dauki mataki domin a sasanta rigimar da ke neman barkewa a PDP
- Shugaban BOT, Walid Jibrin ya tabbatar da cewa an kafa kwamitin da zai zauna da Nyesom Wike
- Atiku Abubakar zai jagoranci kwamitin, zai yi aiki da Gwamnoni da wasu shugabannin PDP na kasa
Abuja - Majalisar amintattu watau BOT na jam’iyyar PDP ta kasa, ta kafa wani kwamitin sulhu da zai yi zama da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Nyesom Wike ya fusata kan yadda aka ki daukarsa a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, Channels TV ta fitar da rahoton.
‘Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ne zai jagoranci wannan kwamiti na sasanci.
Rahoton da aka fitar ranar Lahadi ya nuna kwamitin yana kunshe da gwamnonin jihohin PDP 13.
Walid Jibril ya fitar da jawabi
Shugaban majalisar BOT na PDP, Sanata Walid Jibril ne ya bada wannan sanarwa ta musamman a wani jawabi da ya fitar a ranar 3 ga watan Yuli 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Walid Jibril ya ce za a zauna da Nyesom Wike da zarar Atiku Abubakar da kuma shugaban PDP, Iyorchia Ayu sun gama hutun da suke yi a ketare.
Sauran 'yan kwamitin sulhu
A cewar shugaban wannan majalisa ta amintattu, a kwamitin akwai Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa da kuma Iyorchi Ayu da wasu ‘yan majalisar NWC.
Sauran ‘yan kwamitin sun hada tsofaffin Gwamnoni da Ministoci da aka yi a kasar nan Haka zalika an dauko jagororin jam’iyyar daga jihohi dabam-dabam.
BOT ta yabawa Gwamna Wike
Walid Jibrin ya bayyana Gwamna Wike a matsayin cikakken ‘dan jam’iyya, wanda ya bada gudumuwa sosai wajen ganin PDP ta kawo matsayin da ta ke.
Majalisar BOT ta koka a game da yadda wasu daga cikin ‘yan jam’iyya su ke surutai saboda an zabi IfeanyiOkowa a matsayin mataimakin Atiku Abubakar.
A cewar Sanata Jibrin a siyasa ana samun irin wannan sabani, don haka ne jam’iyya za ta dauki mataki wajen hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyya domin a lashe zabe.
Za mu iya dunkulewa da LP - Kwankwaso
Ku na da labari cewa har yanzu Rabiu Musa Kwankwaso bai cire tsammanin Peter Obi zai iya hakura, ya yi masa ‘dan takarar mataimaki a zabe mai zuwa ba
Saura kusan kwana 10 a gabatarwa hukumar INEC sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da wadanda za su nemi mataimakan shugaban kasa a zaben 2023.
Asali: Legit.ng