Abokin takara : Tinubu na yunkurin daukan Zullum a matsayin mataimakin sa

Abokin takara : Tinubu na yunkurin daukan Zullum a matsayin mataimakin sa

  • Tinubu zai ya bayyana Zullum ko Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar sa nan da kwanaki kadan
  • Wannan ya biyo bayan bukatar manyan yan siyasan Arewa maso yamma na a baiwa Ganduje ko El-Rufa'i
  • Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yana cikin wadanda ake tunanin dauka amma a karshe aka yi watsi da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Dan takarar shuagaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress APC na zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, zai bayyana Kashim Shettima ko Babagana Zullum a matsayin mataimakinsa nan da kwana kadan kamar yadda binciken jaridar Saturday PUNCH rawaito.

Yayin da ya rage kusan kwanaki 12 jam’iyyun siyasa su mika sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da mataimakan takararsu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Tinubu ya mika sunayen yan siyasan guda biyun bayan dogo nazari da shawarwari.

Kara karanta wannan

2023: An Bayyana Sunayen Jiga-Jigan APC 2 Da Tinubu Zai Zabi Mataimakinsa Daga Cikinsu

A jawabin wani makusancin Tinubu, yace shi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yana cikin wadanda ake tunanin dauka amma a karshe aka yi watsi da shi, duk da cewa ya taka rawar wajen ganin Tinubu ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Vanguard
Abokin takara : Tinubu na yunkurin daukan Zullum a matsayin mataimakin sa
Asali: UGC

Jaridar Sunday PUNCH a ranar 26 ga watan Yuni ta ruwaito cewa Tinubu, wanda a halin yanzu yana kasar Faransa, kuma ana sa ran zai dawo kasar nan ba da jimawa ba, domin kammala batun fitar da abokin takara kafin cikar wa’adin, ya takaita bincikensa ne a jihohin Borno, Kano da kuma Kaduna, inda duk yan takarar musulmai ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin APC daga Arewa maso Yamma sun kara kaimi domin ganin yankin ya samar da ‘abokin takara. Jaridar PUNCH ta ruwaito a ranar Juma’a cewa gwamnoni, ‘yan takarar gwamnoni, ministoci da sauran masu ruwa da tsaki daga shiyyar a wani taro da suka yi a Kaduna a ranar Alhamis, sun bayyana aniyarsu ta ingiza manufarsu, ta hanyar amfani da yawan kuri’un yankinsu a matsayin makamin tattaunawa kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Kara karanta wannan

Tinubu ya katange ni daga yakin neman zabensa saboda na janye wa Osinbao - Dr Felix

Sai dai a jawabin wani makusanci Tinubu, ya ce Tinubu zai yi tuntubar karshe akan zabi tsakanin Zulum da Shettima idan ya dawo kasar.

Ana kyautata zaton cewa Zulum ya samu karbuwa sosai a yankin Arewa idan aka yi la’akari da irin nasarorin da ya samu musamman wajen tunkarar rikicin Boko Haram, shi kuma Shettima, aminin Tinubu, ne wanda ya nuna matukar goyon bayan takararsa mussaman lokacin da aka yi kokarin kawo wa takarar sa cikas.

Rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi, mambobi 22 sun buƙaci kakaki ya yi murabus

Rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi kan shugabanci bayan buƙarar mambobin majalisa 22, waɗan da suka kaɗa kuri'ar rashin kwarin guiwa kan kakaki da sauran shugabannin majalisa saboda gazawa.

Idan baku manta ba, ba da jimawa ba Suleiman ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC da aka saɓen shi ƙarkashinta zuwa PDP, hakan ya sa mambobin APC suka koma 16 yayin da PDP ke da 15

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel