Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya fada ma magoya bayansa wanda za su zaba
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ziyarci Port Harcourt, babban birnin jihar Ribas inda ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayan jam’iyyarsa ta APC
- Amaechi ya fadama wadanda suka fusata da kayen da ya sha a zaben fidda dan takarar shugaban kasa da su yayyafawa zukatansu ruwa sannan su zabi jam’iyyarsu
- A cewar Amaechi dole dan takara daya ne zai yi nasara a zaben fidda gwanin inda Allah kuma ya baiwa Bola Tinubu sa’a
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rivers - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bukaci magoya bayansa da su yi aiki don nasarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a babban zaben 2023 mai zuwa.
Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 2 ga watan Yuli, lokacin da dubban magoya bayan APC suka fito don tarbansa a Port Harcourt bayan zaben fidda dan takarar shugaban kasa, jaridar The Nation ta rahoto.
Da yake jawabi ga fusatattun mambobin jam’iyyar wadanda suka sanya ran shine zai lashe zaben fidda gwanin, Amaechi ya ce duk yadda suka kai ga fusata, su hakura su zabi APC, The Cable ta rahoto.
Ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Bari na fara da mika godiya ga dukkanku. Zan yi yar gyara ga jawabin da shugabanmu ya yi. Ba mu yi nasara ba, saboda ko littafin injila da muka karanta ya ce imani ba tare da aiki ba matacce ne. Don haka, za mu yi nasara idan mun shirya yin aiki.
“Zai zama girman kai ne ka zauna a gida sannan ka yi tunanin samun nasara. Ka yi imani da kotuna, za a yi adalci. Kada ku tsorata. Ku je gida sannan ku yi aiki. Aikin mu shine muyi aiki; wannan ne dalilin da yasa na zo. Na zo don mika godiya a gare ku sannan na bukace ku da ku yi aiki. Dukkaninmu shugabanni ne; babu wani shugabannin kananan hukumomi.
“Mu je gida sannan mu yi nasara a yankunanmu. Ya zama dole mu jinjinawa INEC da majalisar dokoki kan rage matakin magudi.
“Zan ta dawowa gida akai-akai don tabbatar da ganin mun yi nasara. Ba zan zama dan siyasar Abuja ba. Za ku dunga gani na a nan don mu yi nasara.
“Dan Allah, zaben shugaban kasa, mu sani cewa ya kamata mu zabi jam’iyyarmu, duk yadda muka kai ga fushi. Ku manta da labaran da kuke ji; ku manta da wadanda ke tsegumi game da wani taro a faransa. Ku bari nan ya zama naku faransan. Ku zabi jam’iyyarku.”
2023: Cikakkun sunayen yan takara da ke fama da batan takardun karatu a fadin jam’iyyun siyasa
A wani labari na daban, mun ji cewa gabannin zaben shugaban kasa na 2023, sabbin abubuwa na ta kunno kai tsakanin yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu.
Kafin yanzu, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a shirinta na tantance yan takara don shiga zaben, ta bukaci masu neman takarar na jam’iyyun siyasa daban-daban su gabatar da wasu takardu don tantancewa.
Sai dai kuma, a inda yawancin yan takara ke samun babban matsala shine wajen gabatar da takardar shaidar karatunsu.
Asali: Legit.ng