2023: Cikakkun sunayen yan takara da ke fama da batan takardun karatu a fadin jam’iyyun siyasa
Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, sabbin abubuwa na ta kunno kai tsakanin yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kafin yanzu, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a shirinta na tantance yan takara don shiga zaben, ta bukaci masu neman takarar na jam’iyyun siyasa daban-daban su gabatar da wasu takardu don tantancewa.
Sai dai kuma, a inda yawancin yan takara ke samun babban matsala shine wajen gabatar da takardar shaidar karatunsu.
A wannan zauren, Legit.ng ta tattaro sunayen wasu yan takara da suke ikirarin bacewar takardunsu.
1. Bola Tinubu
Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki shine kan gaba a wannan rukunin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da aka tambaye shi game da takardar karatunsa, ya ce an sace takardar lokacin da ya yi balaguro a mulkin soji na marigayi shugaban kasa Sani Abacha.
Sai dai kuma, Legit.ng ta rahoto cewa jami’ar Chicago inda ya yi ikirarin ya je karatu ta tabbatar da cewar ya yi wannan jami’ar.
2. Atiku Abubakar
Wani rahoton TheCable ya kuma bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na babban jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) shima yana fama da badakalar takardar karatu.
Kamar yadda wata kafar labarai ta yanar gizo ta rahoto, Atiku a takardar rantsuwa da ya gabatarwa INEC ya ce yana so a san shi da sunansa na yanzu saboda takardar WAEC dinshi na dauke da sunan “Siddiq Abubakar”.
Ya bayyana cewa ya mallaki takardar sakandare a 1965 sannan ya mallaki digiri na biyu a 2021.
3. Abdulmalik Ado Ibrahim
Hakazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Young Progressives Party (YPP), Abdulmalik Ado Ibrahim ma ya yi korafin cewa bai ga ainahin takardar digiri da na diflomansa ba.
Kamar sauran, Ado Ibrahim ya yi rantsuwa a kotu yana mai tabbatar da cewar ya batar da takardun nasa guda biyu.
4. Sani Yabagi
A bangaren dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Democratic Party (ADP), Sani Yabagi, ya bayyana cewa ya sauya sunansa daga “Sani Yusuf” zuwa “Yabagi Yusuf Sani”.
A cewar wani rahoto daga jaridar Nigerian Tribune, Yabagi ya tabbatar da cewar takardun karatunsa daga jami’ar Colombia da WAEC dinsa suna dauke da sunan da.
5. Ifeanyi Okowa
Kamar abokin tafiyarsa Atiku Abubakar, Gwamna Ifeanyi Okowa wanda shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP na fama da badakalar takardar karatu.
Okowa ya aikawa INEC da takardar rantsuwa cewa takardar WAEC dinsa da ya yi a 1974 ta bata.
6. Kabiru Masari
A halin da ake ciki, wanda ke rike da kambun mataimakin shugaban kasa na APC, Kabiru Masari shima ya aikawa INEC da takardar rantsuwa cewa bai ga takardar karatunsa ba.
A takardar rantsuwarsa, ya bayyana cewa takardar karatun nasa ta bata wani lokaci a watan Janairun 2021 yayin da yake hanyarsa ta zuwa Abuja, babbar birnin tarayyar kasar.
Abokin takara : Tinubu na yunkurin daukan Zullum a matsayin mataimakin sa
A wani labarin, dan takarar shuagaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress APC na zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, zai bayyana Kashim Shettima ko Babagana Zullum a matsayin mataimakinsa nan da kwana kadan kamar yadda binciken jaridar Saturday PUNCH rawaito.
Yayin da ya rage kusan kwanaki 12 jam’iyyun siyasa su mika sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da mataimakan takararsu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Tinubu ya mika sunayen yan siyasan guda biyun bayan dogo nazari da shawarwari.
A jawabin wani makusancin Tinubu, yace shi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yana cikin wadanda ake tunanin dauka amma a karshe aka yi watsi da shi, duk da cewa ya taka rawar wajen ganin Tinubu ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Asali: Legit.ng