Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

  • Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers ya saki wani hotonsa daga kasar Turkey tare da rubutu mai dauke da boyayyen sako a shafinsa na Twitter
  • Wike ya saki hoton ne awanni bayan jigon jam'iyyar APC, Joe Igbokwe ya wallafa sako a shafinsa na Facebook inda ya ce gwamnan na Rivers ya gana da Bola Tinubu a Faransa
  • Tun bayan shan kayen da Wike ya yi hannun Atiku Abubakar a zaben fidda gwani na shugaban kasa, jam'iyyar na kokarin shawo kan yayanta don tunkarar zabe a matsayinsu na tsintsinya madaurinki daya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers, wanda ya sha kaye hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya saki magana mai daure kai a dandalin sada zumunta.

A wani wallafa a Facebook a ranar Alhamis, Joe Igbokwe, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi ikirarin cewa Wike ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu a Faransa.

Kara karanta wannan

Kujerar Shugaban PDP na lilo bayan sabon rikicin da ya barke kan abokin takaran Atiku

Nyesom Wike.
Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa. Hoto: @GovWike.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A yayin da suke zagin kowa a dandalin sada zumunta, Gwamna Wike ya tafi Faransa don gana wa da Asiwaju. Zagi, cin mutunci, kiyayya ba tsari bane mai kyau. Sun nuna kiyaya tare da zagin PMB (Shugaba Muhammadu Buhari) tun 2015 yanzu sun koma kan Asiwaju. Za mu jira mu gani," ya rubuta.

Wasu masu amfani da dandalin sada zumunta sunyi watsi da ikirarin na Igbokwe suka bukaci hotuna a matsayin hujja. Bayan wasu lokuta da wallafa rubutun na Igbokwe, an kuma nemi shi an rasa a shafinsa.

Awanni bayan cire rubutun na Igbokwe, Wike a shafinsa na Twitter ya wallafa hotonsa a Turkey da rubutu, "Godiya bisa yammaci mai kyau."

Daily Trust ta rahoto yadda Tinubu ya tafi Faransa bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Villa, Abuja, safiyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga tsaka mai-wuya a 2023, Fayose ya ce har abada Wike ba zai goyi bayansa ba

Awanni bayan Tinubu ya bar kasar, Wike ya saki hotuna inda aka gan shi da takwararsa na Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, a Turkey.

Mataimakin Gwamnan APC Da Ake Rade-Radin Zai Fita Daga Jam'iyyar Ya Yi Karin Haske

A wani rahoton, Mataimakin gwamnan Jihar Ebonyi, Kelechi Igwe, ya ce ba ya shirin ficewa daga jam'iyyar APC zuwa Labour Party.

Hadiminsa, Monday Uzor, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abakaliki, Premium Times ta rahoto.

Wani rahoto da aka wallafa a dandalin sada zumunta ya ce Mr Igwe ya kammala shirin fita daga APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164