Abinda Muka Tattauna da Obasanjo Yayin da ya Kawo Min Ziyara, Ango Abdullahi

Abinda Muka Tattauna da Obasanjo Yayin da ya Kawo Min Ziyara, Ango Abdullahi

  • Shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya sanar da abinda suka tattauna da Obasanjo a ziyarar da ya kai masa a Zaria
  • Ango Abdullahi ya sanar da cewa sun tattauna kan siyasar Najeriya ne da kuma makomar kasar a yayin da take tunkarar zaben 2023
  • Ango yace duba da sanin irin aikin da Tinubu da Atiku zasu iya, baya hango shawo kan matsalolin kasar nan a tattare da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zaria, Kaduna - Shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, yace halin da siyasar Najeriya ke ciki shi ne jigon tattaunawarsa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ziyarar da ya kawo masa Zaria, jihar Kaduna.

Abdullahi, tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar da yayi da Daily Trust a Zaria.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar matasan APC sun dage, sun ce Zulum ne ya kamata ya yi takara da Tinubu

Farfesa Ango Abdullahi
Abinda Muka Tattauna da Obasanjo Yayin da ya Kawo Min Ziyara, Ango Abdullahi. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC
Yace: "Abu na farko da tsohon shugaban kasar yace shine 'Muna tunkarar sabon shugabancin da zai fitar da mu daga kalubalen da suka yi wa kasar nan katutu, saboda akwai ra'ayoyi daban-daban kan ko kasar nan tana kan hanyar tsira ko a'a?'
"Sai dai kuma, akwai alamun muna da ra'ayi daya game da 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasa dake neman shugabancin kasar nan. Duka mun yarda Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar basu da yadda zasu yi da matsalolin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan ce matsayata kuma ina kan ta.
"Duk da wannan ra'ayina ne, na kafa su ne saboda na dogara da dalilan cewa na san su da kyau tare da sanin ayyukansu. Bana tunanin suna da yadda zasu shawo kan matsalar kasar nan."

Abdullahi yace akwai 'yan takara 15 daga jam'iyyun siyasa dake kokarin hayewa wannan kujerar, 'yan Najeriya zasu iya duba wani daga ciki.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

A matsayar dattijon arewa, Abdullahi yace arewa tafi mayar da hankali a bangaren ingancin shugabanci ba tare da duban daga inda ya fito ba.

Yace muna fatan wannan ingantaccen shugabanci zai zo daga arewa.

2023: Makomar 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu a Jihohi 19 na Arewacin Najeriya

A wani labari na daban, yayin da ake jiran zuwan ranar zaben shekarar 2023, wasu sanatotin jam'iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyun adawa.

Yawancin idan ba duka wadanda suka sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC sun sauya sheka bayan gaza samun tikitin tsayawa takara domin cigaba da tabbata a madafun iko ko tsayawa takarar gwamna a zaben shekarar 2023.

Idan an kula, wannan ne karo na farko da jam’iyyar ta tsayar da dan takarar shugaban kasarta daga yankin kudu.

Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne, ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da kuri’u 1,271 bayan an yi zaben a ranar 8 ga watan Yuni yayin da ya kayar da ‘yan takara 13, 7 kuma su ka janye tare da mara masa baya a filin zaben.

Kara karanta wannan

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng