2023: Kungiyar matasan APC sun dage, sun ce Zulum ne ya kamata ya yi takara da Tinubu

2023: Kungiyar matasan APC sun dage, sun ce Zulum ne ya kamata ya yi takara da Tinubu

  • Wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun bayyana cewa Gwamna Babagana Zulum ne ya fi dacewa a matsayin abokin takarar Bola Tinubu a zaben 2023
  • Masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa hadakar za ta karawa jam’iyyar APC tagomashi a zaben da za a yi shi ne ba Zulum dama
  • Sun kuma bayyana cewa tikitin Tinubu/Zulum zai karawa jam’iyya mai mulki dama a zaben shugaban kasa mai zuwa ko a dace a lashe zabe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Kungiyoyin matasa da dama na APC a jihar Bauchi, sun yi kira ga shugabannin jam’iyyar da mai rike da tutar shugaban kasa a zaben 2023, Bola Tinubu da su zabo Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a matsayin abokin takararsa, rahoton Punch.

Shugaban kungiyar matasan na APC, Malam Shamsuddeen Waziri wanda ya yi wannan kiran ya ce Tinubu da Zulum za su kara wa jam’iyyar riba a zabuka da kuma kara mata damar lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Dogara ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu – Kungiya ga APC

Zulum ne ya cancanci zama abokin tafiyar Tinubu
2023: Wasu kungiyoyin APC sun dage, sun ce Tinubu kamata ya yi ya zabo Gwamna Zulum | Hoto: Borno state government
Asali: UGC

Kungiyar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a Bauchi, inda ta ce bayan nazarin matsalolin tsaro da tattalin arziki da sauran matsalolin da suka dabaibaye Najeriya, sun ba da shawarin a zabi Zulum domin tafiya da Tinubu.

Da yake karin haske ga batun, Shamsuddeen ya ce Zulum ya fi karbuwa a idon ‘yan Najeriya fiye da duk wani wanda zai yi takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, Leadership ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa irin nasarorin da gwamnan ya samu da kuma tsarin shugabancinsa nagari a cikin shekaru uku da suka gabata, sun sanya shi zama a zukatan al’ummar Borno da ma ‘yan Najeriya baki daya.

A cewar kungiyar;

“Don haka mu shugabannin matasan jam’iyyar APC na Bauchi, muna kira ga shugaban jam’iyyarmu ta kasa, kuma mai rike da tutar jam’iyyar, da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, da mu yi la’akari da kiran da muka yi na cewa ba wai kawai a tsayar da dan takarar mataimakin shugaban kasa daga Arewa maso gabas ba a zabo Zulum a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Jigon siyasa: Kada Igbo su bata kuri'a wajen zaban Atiku, su zabi Tinubu saboda wani dalili

A wani labarin, Amb Ginika Tor ta yi kira ga al’ummar yankin kudu maso gabas da kada su yi kuskuren zaben jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Wakiliyar ta jihar Enugu a hukumar da’a ta tarayya ta ce jam’iyyar PDP ba ta cancanci kuri’un kabilun Igbo ba, saboda kin amincewar jam’iyyar na ba da tikitin takarar shugaban kasa a yankin kudu maso gabas, inji rahoton jaridar The Nation.

Ta ce a maimakon goyon bayan Atiku tare da kada masa kuri'u, ya kamata dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shahara ya kuma mamaye kuri'un yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel