Yanzu-Yanzu: Gwamna Uzodinma ya zargi kundin INEC da jawo cece-kuce kan karatun Tinubu

Yanzu-Yanzu: Gwamna Uzodinma ya zargi kundin INEC da jawo cece-kuce kan karatun Tinubu

  • Gwamnan jihar Imo ya zargi hukumar zaɓe da haddasa duk abinda ya biyo baya game da takardun shaidar karatun Bola Tinubu
  • Gwamna Hope Uzodinma ya ce tun shekarar 1999 Tinubu ke shiga zaɓe a Najeriya kuma takardun nan ba canzawa suke ba
  • Ya kuma ba da tabbacin cewa jam'iyyar APC zata zaɓo mataimakin ɗan takararta na shugaban ƙasa kafin lokaci ya ƙare

Abuja - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya zargi asalin garken aje bayanan hukumar zaɓe INEC da haddasa cece-kuce da gardamar da ta biyo baya kan takardun karatun Bola Tinubu.

A cewarsa, duk ba zata faru da ɗan takarar shugaban kasa na APC game da shaidar karatunsa ba inda INEC na da kundin aje bayanai mai aiki, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'A haife shi a 1958, ya fara makaranta 1959?' Sabbin matsaloli da suka taso kan takardun sabon shugaban Alkalai

Bola Ahmed Tinubu ya bar wurin karatun Firamare da na Sakandire a Fom ɗin INEC da ya cike CF 01 na zaɓen 2023 da ke tafe.

Shugaba Buhari da gwamna Hope Uzodinma.
Yanzu-Yanzu: Gwamna Uzodinma ya zargi kundin INEC da jawo cece-kuce kan karatun Tinubu Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

Sai dai hakan ya haddasa babbar taƙaddama da cece-kuce, inda yan Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta suka fara tantama kan gaskiyar Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da yake zantawa da manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan gana wa da shugaba Buhari, Uzodinma ya bayyana yaƙinin cewa za'a warware batutuwan da suka baibaye takardun Tinubu.

Vanguard ta ruwaito Gwamnan ya ce:

"Duk waɗan nan abubuwan kalubale ne da suka shafi jam'iyya da za'a warware su. Amma game da ɗan takarata na shugaban kasa, bai kamata a ɗaga magana kan takardunsa ba."
"A 1999 ya shiga zaɓe ya zama gwamnan Legas, a 2023 ya shiga zaɓe ya zarce a kujerar gwamnan Legas. Ya lashe zaɓen Sanata a ƙasar nan, idan ana aje bayanai, kundin INEC na aiki, ba sai ya sake miƙa takardunsa ba."

Kara karanta wannan

Babbar Kotu ta ba da Belin ɗan majalisar tarayya bayan shafe kwanaki 62 a tsare

"Duk abinda ake buƙata, lokaci bai ƙure ba, ina da tabbacin kafin lokaci ya ƙare, zai miƙa duk abinda ake buƙata."

Shin har yanzun APC na da kwarin guiwar lashe zaɓe?

Yayin da aka tambaye shi ko yana ganin har yanzun APC ce jam'iyya mai nasara duk da wahalar zaɓo mataimakin Tinubu, gwamnan ya ce:

"Me kuke nufi da wahala? Waya faɗa muku? Har yanzun lokaci bai wuce ba, sai lokacin kai sunayen ya ƙare kuma muka gaza zaɓo ɗan takarar mataimaki, a nan ne kaɗai zaku yi mana tambaya irin wannan."
"Na san saboda ƙarfin jam'iyyar mu kasancewarta mai mulki da kuma amfanin APC a wurin mu da ku baki ɗaya, Na yaba da nuna damuwar ku, amma ina tabbatar muku da cewa zamu cike cikakken tikiti a zaɓen shugaban kasa."

A wani labarin kuma Gwamna Wike, Tambuwal, Diri da sauran jiga-jigan da zasu jagoranci yaƙin neman zaɓen PDP a jihar Osun

Kara karanta wannan

Takardun makarantar da Atiku, Tinubu, Kwankwaso da Obi suka gabatarwa hukumar INEC

Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta kafa tawagar yaƙin neman zaɓe da zasu yi jagoran Kanfen na zaɓen gwamnan jihar Osun wanda zai gudana ranar 16 ga watan Yuli, 2022.

Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, shi ne zai jagoranci tawagar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar, yayin da wasu gwamnoni 11 zasu mara masa baya a matsayin mambobi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel