Osun: Gwamna Wike, Tambuwal, Diri da sauran jiga-jigan da zasu jagoranci Kanfen PDP

Osun: Gwamna Wike, Tambuwal, Diri da sauran jiga-jigan da zasu jagoranci Kanfen PDP

  • Yayin da ake gab da fita fafata zaɓen gwamnan Osun, jam'iyyar PDP ta kafa tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takararta
  • Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ne zai jagoranci tawagar yayin da gwamnoni 11 zasu mara masa baya a matsayin mambobi
  • Sakataren tsare-tsare na PDP, Umar Bature, a wata sanarwa, ya ce za'a kaddamar da tawagar ranar Laraba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta kafa tawagar yaƙin neman zaɓe da zasu yi jagoran Kanfen na zaɓen gwamnan jihar Osun wanda zai gudana ranar 16 ga watan Yuli, 2022.

Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, shi ne zai jagoranci tawagar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar, yayin da wasu gwamnoni 11 zasu mara masa baya a matsayin mambobi.

Tutar jam'iyyar PDP.
Osun: Gwamna Wike, Tambuwal, Diri da sauran jiga-jigan da zasu jagoranci Kanfen PDP Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Umar Bature, ya fitar.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takarar gwamna da wani babban jigon PDP sun sauya sheka zuwa NNPP mai kayan daɗi

Gwamnonin da suka shiga tawagar a matsayin mambobi sun haɗa da, Nyesom Wike (jihar Ribas), Seyi Makinde (Oyo), Aminu Tambuwal (Sokoto), Okezie Ikpeazu (Abiya), Udom Emmanuel (Akwa Ibom), da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran gwamnonin sune; Darius Ishaku (Taraba), Samuel Ortom (Benuwai), Godwin Obaseki (Edo), Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa) da kuma Bala Mohammed (jihar Bauchi).

Jiga-Jigan PDP da suka shiga tawagar

Sauran jiga-jigan PDP da suka shiga cikin tawagar sun haɗa da Sanata Tanimu Philip Aduda, Anbasada Taofeek Arapaja, Bukola Saraki, Olusegun Mimiko, Sanata Samuel Anyanwu, Chief Dan Orbih, Debo Ologunagba, Dino Melaye, da sauran su.

Sanarwan ta ƙara da cewa za'a kaddamar da tawagar ranar Laraba kuma ta roki mambobin kwamitin shugabanni na PDP ta ƙasa baki ɗaya da su halarci wurin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya tafi ƙasar Faransa yin wasu muhimman abubuwa

A wani labarin kuma Yayin da APC ke kokarin ɗinke barakar majalisa, Wani Sanata ya fice daga jam'iyyar

An sake samun karin wani Sanatan APC da ya tabbatar da barin jam'iyyar duk da yunkurin sasanci da ɗinke ɓarakar cikin gida.

Sanatan mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta arewa, Godiya Akwashiki, ya ce mutanen mazaɓarsa sun jima suna matsa masa lamba kan ya sauya sheka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel