2023: Dattawan Kudu da Arewa za su fadi wanda ya kamata su zaba cikin 'Yan takara 7

2023: Dattawan Kudu da Arewa za su fadi wanda ya kamata su zaba cikin 'Yan takara 7

  • Southern and Middle Belt Leaders Forum (SMBLF) ta nuna za ta tsoma bakinta a game da zaben 2023
  • Kungiyar za ta fadawa mutane wa ya kamata su ba kuri’arsu a zaben shugaban kasa tsakanin 'Yan kudu
  • An yi wannan zama ne da irinsu Janar Zamani Lekwot, Victor Attah, da Chukwuemeka Ezeife a garin Abuja

Abuja - Tribune ta ce shugabannin kungiyar nan ta SMBLF sun tattauna a garin Abuja a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni 2022 a game da batun kasa.

Kungiyar ta ce za su zauna da ‘yan siyasan da suka tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023, domin su fitar da wanda mutane za su marawa baya.

Wannan bayani yana cikin jawabin da SMBLF ta fitar a karshen zaman da aka yi, kungiyar ta soki duk jam’iyyun da suka tsaida ‘dan takararsu daga Arewa.

Kara karanta wannan

Jerin manya 6 da suka yi wa Peter Obi mugun baki, su ka ce ba zai mulki Najeriya a 2023 ba

Jaridar The Cable ta rahoto SMBLF ta na mai cewa ya kamata wanda zai zama shugaban kasa a Mayun 2023 ya fito ne daga yankin kudancin Najeriya.

A dalilin haka aka ji kungiyar ta na godewa jam’iyyun APC, AAC, ADC, APGA, LP, PRP da SDP da suka tsaida ‘dan takararsu na shugaban kasa daga kudu.

PDP, NNPP sun kai takara Arewa

Hakan yana nufin wannan kungiya ta mutanen Kudu da tsakiyar Najeriya ta yi Allah-wadai da jam’iyyun adawa na PDP, AA, ADP, APM, YPP da NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin kungiyar za su tattauna da ‘yan takaran APC, AAC, ADC, APGA, LP, PRP da SDP ne kurum, domin gane wanda ya fi dacewa su ba goyon baya.

SMBLF
Wani taron kungiyar SMBLF Hoto: www.thenigerianvoice.com
Asali: UGC

Shirin katin zabe na kasa

A jawabin bayan taron, SMBLF ta ce tana duba kokarin da hukumar INEC ta ke yi na rajistar katin zabe, ta yi kira ga wadanda suka kai 18 su mallaki katin PVC.

Kara karanta wannan

Kayan marmari: Jam'iyyar su Kwankwaso NNPP ta samu mutane miliyan 2 a jihar Borno

Wadanda suka halarci taron sun yi kira da babbar murya ga hukumar zabe da ta dage wajen ganin an yi wa kowane ‘dan Najeriya da ya cancanta rajista.

A game da sha’anin rashin tsaro da ake fama da shi, kungiyar ta bukaci gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo karshen halin bakar wahalar da ake ciki a yau.

Kashe-kashe da matsalar tsaro

Jawabin da SMBLF ta fitar ya hada da Allah-wadai da kashe masu ibada da aka yi a cocin garin Owo a jihar Ondo, da rikicin da ake yi a Kajuru a jihar Kaduna.

Ganin an yi kwanaki 89 da dauke mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna, kungiyar ta ce akwai bukatar a kubutar da duka wadanda ke hannun ‘yan bindiga.

Shugabannin Neja-Delta, Afenifere, Ohanaeze; Edwin Clark, Ayo Adebanjo, Dr Pogu Bitrus, da Okey Emuchay su ka sa hannu a takardar da aka fitar bayan taron.

Ango ya soki Atiku da Tinubu

Kara karanta wannan

Uwargidar Najeriyar gobe: Labarin Matan Tinubu, Atiku, Peter Obi da na Kwankwaso

Ku na da labari cewa daya daga cikin dattawan Arewa, Ango Abdullahi ya tofa albarkacinsa a game da manyan ‘yan takarar shugaban kasa na zaben 2023.

Dattijon ya nuna babu abin da Bola Tinubu da Atiku Abubakar za su iya tabukawa, ya ce Yemi Osinbajo da Mohammed Hayatuddeen za su fi cancanta da mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel