Jerin tsofaffin Gwamnonin jihohi 28 da za a iya gani a zauren Majalisar Dattawa a 2023
- Akwai Gwamnoni masu-ci da-dama da ake tunanin za su zama Sanatoci a Majalisar Dattawa a zaben 2023
- Wadannan Gwamnonin jihohi za su hadu da wasu tsofaffin Gwamnonin Najeriya da yanzu suke Majalisa
- Idan Gwamnonin sun samu yadda suke so, za a cika Majalisar Dattawa da mutum 28 da sun taba rike Jihohinsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Jaridar Premium Times ta kawo wani dogon rahoto da ya bayyana cewa majalisar dattawan kasar nan ta zama matattarar tsohon Gwamna.
A halin yanzu akwai tsofaffin gwamnoni 14 daga Kudu da Arewacin Najeriya da ke rike da kujerar Sanatoci, Wasu gwamnoni masu-ci kuma su na harama.
Akwai tsofaffin Gwamnonin da yanzu Sanatoci ne da suka rasa takara, a dalilin haka ne suka sauya-sheka, irinsu Ibrahim Shekarau da Adamu Aleiro.
A zaben 2023, zai yiwu a samu tsofaffin gwamnoni 28 da wadanda wa’adinsu zai kare a 29 ga watan Mayu da za a rantsar a matsayin Sanatoci a majalisa.
Sababbin shiga
Rahoton ya ce tsofaffin gwamnonin da yanzu su ke harin zama Sanatoci a kasar sun hada da:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Adams Oshiomhole
2. Dave Umahi
3. Aminu Tambuwal
4. Darius Ishaku
5. Samuel Ortom
6. Okezie Ikpeazu
7. Abubakar Sani Bello
8. Ibrahim Danwkambo
9. Abdulaziz Yari
10. Ifeanyi Ugwuanyi
11. Simon Lalong
12. Gbenga Daniel
Tsofaffin hannu
Jaridar ta ce tsofaffin Gwamnonin da suke kokarin zarcewa a kujerar majalisar dattawa:
13. Aliyu Wammako
14. Kabiru Gaya
15. Chimaroke Nnamani
16. Umar Al-makura
17. Danjuma Goje
18. Orji Kalu
19. Kashim Shettima
20. Ibrahim Gaidam
21. Seriake Dickson
22. Saminu Turaki
23. Gabriel Suswan
24. Ibrahim Shekarau
25. Adamu Aliero
26. Sam Egwu
27. Atiku Bagudu
28. Godswill Akpabio
Abin ya zama al'ada
Wani rahoto da mu ka fitar kwanakin baya, ya nuna cewa yanzu haka akwai tsofaffin gwamnoni fiye da 15 da su ke rike da kujera majalisar dattawa a Najeriya.
A zaben da za ayi a 2023, akwai wasu gwamnoni da wa’adinsu zai kare da za su yi takarar Sanata. Za a samu wannan a Sokoto, Benuwai, Filato da watakila Ebonyi.
Asali: Legit.ng