2023: Zulum Muke So Ya Zama Mataimakin Tinubu, Masu Ruwa Da Tsaki a APC

2023: Zulum Muke So Ya Zama Mataimakin Tinubu, Masu Ruwa Da Tsaki a APC

  • Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na son jam'iyyar ta zabi Gwamna Zulum na Borno a matsayin mataimakin Tinubu a 2023
  • Abdullahi Aliyu Katsina, jagoran masu ruwa da tsakin ne ya bayyana hakan a Minna yana mai cewa sun yi kuri'ar jin ra'ayin al'umma a jihohin arewa 19 kuma Zulum ne ya fi karbuwa wurin mutane
  • Katsina ya ce mutanen Jihar Borno suna son Zulum ya yi tazarce don cigaba da ayyukan alheri da ya fara amma hidimar da zai yi wa kasarsa ya fi hakan muhimmanci

Minna, Niger - Jagoran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga Arewa, Abdullahi Aliyu Katsina ya ce kuri'an jin ra'ayin al'umma da kungiyar ta yi ya nuna cewa zaben gwamnan Borno, Babagana Zulum ne kadai a matsayin mataimakin Ahmed Bola Tinubu zai tabbatarwa APC samun nasara cikin sauki.

Kara karanta wannan

Jerin manya 6 da suka yi wa Peter Obi mugun baki, su ka ce ba zai mulki Najeriya a 2023 ba

Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno.
2023: Masu Ruwa Da Tsaki A APC Na Son Zulum Ya Zama Mataimakin Tinubu. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Katsina, yayin taron manema labarai da aka yi a jiya a Minna ya ce duk da cewa mutanen Borno ba su son ya tafi saboda ayyukan alheri da ya ke yi a jihar, yi wa kasa hidima zai fi dacewa, Leadership ta rahoto.

Mutanen jihohin arewa 19 Zulum suke so, In ji Katsina

"Abin da ke gaban mu shine yadda APC za ta cigaba da rike mulki bayan zaben 2023. Cin zaben fidda gwani nasara ce guda kuma cin babban zabe wani nasara ne mai muhimmanci. Kuri'ar jin ra'ayin da muka yi ya nuna karara Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno shine mutumin da mafi yawancin masu zabe a arewa suka amince da shi a yau.
"Mun yi kuri'ar jin ra'ayin masu zabe a jihohi 19 na Najeriya; Da kallubalen da ke gabanmu na dan takarar PDP daga arewa, wa zai iya samarwa APC nasara? Amsar ita ce Gwamna Zulum," Katsina ya kara.

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

Ya ce abin da ya fi muhimmanci shine cin zaben 2023 amma ya zama dole a tsayar da mutum wanda ake mutunta shi, ake sonsa, an yarda da shi domin ya kawo kuri'un arewa kuma Zulum ne kadai ke da wannan halayen.

Jagoran kungiyar ya ce a halin yanzu ana bukatar dukkan yan jam'iyya su jajirce su yi aiki domin ganin jam'iyyar ta yi nasara a babban zaben 2023.

Legit Hausa ta tuntubi wani mai nazarin harkokin siyasa mazaunin Kano, Malam Kabiru Bala, domin jin ra'ayinsa game da zaben Zulum da masu ruwa da tsakin na APC ke son a yi a matsayin mataimakin Tinubu.

Malam Bala ya ce yana ganin zaben Zulum zai fi bawa jam'iyyar ta APC daman cin nasarar zaben duba da ayyukan da ya yi a jiharsa idan aka kwatanta da sauran duk da korafi kan tikitin musulmi da musulmi da wasu ke yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shahararren 'Dan kasuwan Najeriya ya ba takarar Peter Obi kwarin gwiwa

"Duk da cewa tikitin musulmi/musulmi zai tada kura a siyasance, ina kyautata zaton wannan zabin Zulum zai fi dacewa fiye da sauran idan aka yi la'akari da ayyukansa," in ji Bala.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164